✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha Zuwa Ga Maza (6)

Babu wata riga da matan Hausawa za su sa ta taimaka wajen kawo sauki ga irin wannan rayuwa irin ta zurfafa ko kaurara iliminsu, na…

Babu wata riga da matan Hausawa za su sa ta taimaka wajen kawo sauki ga irin wannan rayuwa irin ta zurfafa ko kaurara iliminsu, na addini da na zamani. Rashin yin haka shi ne babban tarnakin da ke gaban hukuma da masu fada-a-ji. Rashin kula da aiwatar da tsare-tsare kan haka, na daga cikin abin da ya jefa su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu irinsu da dama cikin rayuwar jangwam! Labarinsu, tamkar labarin yawancin matan Hausawa ne, Malam!”

Na dade ina nazarin wadannan bayanai da wannan mata ke turowa, ina kuma samun natsuwa da ganin yadda take tafe tana kafa hujja da misalai, domin tabbatar da batutuwan da take bayyanawa. A duk lokacin da nake zaune ni kadai ina nazarin abubuwan da take aiko min sai in kara fahimtar babban dalilinta na turo mini jawaban da kuma dalilan bayyana abin da ke cikin kwakwalwarta, ba kunya, ba jin tsoro, ba fargabar za a ce wannan wace irin mace ce daga cikin matan Hausawa? Bisa wannan tunani ne ya sa na zauna na aika mata da dogon bayani game da dalilan da suka sa na kyale ta, ita kadai ke zuba, ni kuwa sai dai zuba hajar zomo da na yi, kuma ba wai don ba ni da abin cewa ba ne, abin nan ne da ake fada game da hararwa, wato sauki ce ga cikin da ya lalace, idan ba ta amaye abin da ke cikinta ba, to kuwa ba za ta samu lafiya ba.

A cikin wani dare ne na aika mata da sako nake cewa, “Daga abin da muka tattauna a tsawon lokaci na fahimci lallai kina da madafai masu yawa a wannan batu, amma zan bar nawa sharhin sai kin dire. Sai dai kafin ki bayyana mini batun su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu irinsu da dama da kika ce rayuwarsu tamkar rayuwar dukkan matan Hausawa ne, ba kya jin cewa akwai wadanda daga cikin matan Hausawan nan da ke zaune cikin aljannar duniya? Ba kya jin cewa akwai irinki da suka samu sukuni da dama suna gudanar da rayuwarsu yadda ta dace, sanye da rigunan da kika bayyana tun farko da za mu iya bayar da misali da su, maimakon mu tsaya wuri guda muna kallon wadanda ke cikin tasku da ni-’ya su? Ba kya jin cewa akwai kuma wadanda suka kasance sanye da rigunan nan da kike ta tokabo da su, amma kuma ba su tsinana wa al’umma komai ba? Ba kya jin cewa akwai daga cikin matan Hausawa da kuma ba su sa wadannan riguna ba, amma kuma suna cikin jin dadi da walwala fiye da wadanda suka sanya rigunan da kike ta kakabi a kai? Ba kya jin fyadar ’ya’yan kadanya da kike yi, ba zai kawo mafita ba a cikin wannan lamari?”

Saboda al’amuran da suka sha min kai, na manta da wannan tattaunawa da muke yi da wannan mata na kusan kwana biyu. Ban kula ba ashe tana ta aiko da sakonni har ta fara tunanin ko na yi watsi da ita ce ko kuma bayanan nata ba su gamsar da ni ne ba. Ran nan da tsakar dare kamar an tsunkule ni sai na shiga cikin akwatin ajiye sakonni, abin da na fara cin karo da shi bai ba ni mamaki ba, dogon sharhi cike da magiya da ban-magana daga gare ta. Tana cewa da ni, “Allah Ya gafarta Malam! Na san na yi kutse inda bai kamata na kutsa ba, na kuma san cewa ban kai matsayin da zan tsaya kafada-da-kafada da kai ba, domin in yi musayar ra’ayi, ko kusa, amma in har ka rufe ni a nan, ba ka kyauta mini ba, domin kuwa abubuwan da ke shakure a cikin rayuwata ba su kimsuwa haka nan, sai na amayar da su. Suke ni suke yi, kuma ina da yakinin ba wanda zan iya bayyana wa abubuwan nan ya fahimce ni a wannan fage da muke ciki, kamarka. Ka taimaka ka saurare ni, domin na tabbata ta haka labarina da labarin ’yan uwana masu rayuwa cikin tasku zai isa inda ya kamata ya isa. Ta haka labarin su Maryam da Halima da Indo A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu irinsu da dama zai samu fita fili, ba kuma don a samar da mafita ba, domin a san suna nan, rayuwa ce kurum, tamkar ya babu.”

A sakonta na gaba ta ci gaba da cewa, “Maryam da nake magana, ita ce kila amsar daya daga cikin batutuwan da ka lissafo a can baya. Ta dai yi karatun addini gwargwado, tun tana karama, ta kuma yi karatun firamare da sakandare daga baya. Ta kuma dora daga nan ga bisa zurfafa karatun addini har ta shiga jami’a. Ta kammala karatun jami’a, aka yi mata aure. Ta yi hidimar kasa ta kuma ci gaba da rayuwar aurenta. Ta samu albarkar aure gwargwado, amma cikin tsarin Ubangiji bayan kusan shekara 20 da aure, kwatsam mijin nan ya shiga cikin gonar isa, saboda kurum yana son kara aure, ya saki Maryam, ya sallame ta, ta koma gidan iyayenta. Ga manyanci ya shige ta, ga ta ba wata sana’a da ta koya a cikin tsawon shekara 20 na bautar aure. Duk zamanta da mijin nan ba abin da yake nuna mata sai ba ta bukatar karo karatu ko yin wani aiki don ta yi digiri, domin yana dauke mata nauyin da ke wuyanta, na ci da sha da matsuguni. Haka suka yi wannan rayuwa, amma ga ta yanzu cikin rana tsuru-tsuru! Ita ba iyaye gare ta ba, domin sun riga mu gidan gaskiya, ba wani jigo ya rage mata ba daga cikin yayye da kanne, zaune take kurum a gidan gado, ba abin da take nomawa sai takaici da bacin rai. Maryam ba aikin yi, bare sana’ar dorarwa. Maryam ba jari ko wani abin dogara da kai, sai taimako daga wadanda suka tuna da ita a gidan gado. Neman aiki da tsohon satifiket na digiri ya zame mata matsala, kananan mata ma yaya suka kare bare ita mai kusan shekara 43 a rayuwa. A halin da take ciki, ba abin da ya raba Maryam da almajira, duk  da ta sa dukkan rigunan da nake magana a baya! Don Allah Malam ina laifin Maryam a nan? Ina mijin nata yanzu? Yana can zaune da wadansu sababbin mata da ya aura bayan ya kori Maryam, duniya ta koma masa sabuwa! Nawa ne irin Maryam ke raye yanzu ko makamantan irinta da ba mu damu da halin da suke ciki ba?”

Za mu ci gaba