✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDE ta koyar da matasa 1000 sana’o’i a Jigawa

Hukumar NDE ta bai wa matasa 1000 horo sana’o’in hannu inda aka koya musu yadda za su yi man shafawa da sabulun wanki da turare…

Hukumar NDE ta bai wa matasa 1000 horo sana’o’in hannu inda aka koya musu yadda za su yi man shafawa da sabulun wanki da turare da kafinta da kanikanci da walda da sauransu.

Alhaji Sani Lawan daya daga cikin manyan daraktocin Hukumar NDE ya ce an zakulo wadanda aka horar din ne daga daukacin kananan hukumomin jihar guda 27.

Ya ce makasudin bai wa matasan horon shi ne a samar wa matasa abin yi su zama màsu dogaro da kansu.

Alhaji Sani ya kara da cewa bayan horar da ake musu, za a rika basu alawus na Naira dubu biyu.

Yayinda mata za su yi mako biyu wajen samun koyon sana’ar, su kuma mazan za su yi wata uku ne.

Daga nan sai ya hori matasan su zama masu neman ilimi domin sai da ilimine ake samun cigaban rayuwa, sannan ya bukaci su yi amfani da irin abin da suka koya a matsayin sana’ar da za su iya rike kansu.

Ya ce da zarar matasan sun kammala samun horon, NDE zà ta ba su kayan aiki kuma za ta ba su jarin da za su fara, sannan za su sanya idanu a kansu domin ganin sun ci gaba yin sana’ar da aka koya masu, sannan ya yi gargadin cewa duk wanda suka samu ya sayar da kayan sana’ar da suka bashi sai ya biya, domin ba za su amince da hakan ba.

A karshe sai ya hores u su zama mutane na gari, inda ya nuna takaicinsa a kan yadda zaman banza ya yawaita a tsakanin matasan Arewa.