✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama masu safarar kwayoyi 15 a Kaduna 

Kwamandar Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) na Kaduna Bala Fage, ya bayyana cewa Hukumar ta yi nasarar kama mutum 15 a…

Kwamandar Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) na Kaduna Bala Fage, ya bayyana cewa Hukumar ta yi nasarar kama mutum 15 a cikin watan Satumba da muke ciki da zargin safarar kwayoyi a Kaduna.

Ya kuma ce, mutanen da aka kama dukkaninsu a cikin watan Satumba ne kuma a garuruwan Zariya da Kafanchan da Saminaka da cikin garin Kaduna aka kama su.

A cewarsa, kwayoyin da aka samu a hannunsu wanda sun hada: da tabar wiwi da Tramadol da sauran su idan aka yi kiyasin kudin su zai kai Naira miliyan 100.

“Yawancin kwayoyin da muka kama a Zariya da Kafanchan da Saminaka da kuma cikin garin Kaduna ne. Sannan a yanzu haka mun kama mutum 15. Zan iya cewa, wannan sashe namu ya samu babbar masara a cikin watannan na Satumba.

“Abin da muke cewa, a kullum shi ne idan aka bari wadannan kwayoyi suka yadu cikin al’umma Allah kadai Ya san halin da matasan mu zasu tsinci kansu musamman masu ta’ammali da miyagun kwayoyi. Muna kuma shawartar iyaye da su rika sa ido akan ‘ya’yansu da kuma irin mutanen da suke mu’amala da su,” in ji shi.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar a bisa taimako da goyan baya da take baiwa hukumarsa a yakin da take yi da miyagun kwayoyi a jihar.

Kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan shi ma ya yaba da ayyukan hukumar a jihar da kuma nasarar da ta samu a cikin watan Satumbar da muke ciki.