Da Dumi Dumi

NFF ta dage ’yan kwallon da suka hada baki aka yi coge a shiyyar Bauchi har tsawon rayuwarsu

Alhaji Aminu Maigari Shugaban Hukumar NFFHukumar kula da shirya wasan kwallon kafa ta kasa da aka fi sani da NFF, a ranar Litinin da ta gabata ne ta bayar da sanarwar dage kungiyoyin kwallon kafa guda hudun nan da suka hada baki aka tashi wasa da ci 67-0 da 79-0 a shiyyar Bauchi.
Idan za a tuna, kimanin makonni biyu ne hukumar ka kafa kwamitin bincike bayan da dakatar da kungiyoyin kwallon kafar na wucin-gadi kafin a kammala bincike don haka yanzu hukumar ta yi musu hukuncin da yakamace su kenan.
A yayin wasan, kungiyar kwallon kafa ta Filato United Fedders ce ta lallasa ta Akurba United da ci 79-0 yayin da ta Police Machine ta yi kaca-kaca da ta Bubayero da ci 67-0.
A binciken da hukumar kwallon kafar ta yi, ta gano cewa daukacin ’yan kwallon da jami’ansu da kuma alkalan wasa da mataimakansu sun hada kai ne wajen yin wannan aika-aika da ta janyo wa kasar nan surutu a ciki da wajen kasa.
Mataimakin Shugaban Hukumar Mike Umeh ya kara da bayani a lokacin da yake hira da manema labaraia Abuja cewa, “abin kunya ne a ce dan kwallo ya zura kwallaye guda 11 shi kadai yayin da a wasa na biyu aka zura kwallo hudu a cikin minti daya.  Haka kuma an samu dan kwallon da ya zura kwallo uku a ragarsa da gangan da haka ya nuna ko shakka babu an hada baki don yin coge ne”.
Kwamitin da hukumar NFF ne ya bayar da shawarar a dage kulob-kulob hudun da suka buga gasar har tsawon shekara goma ba tare da sun shiga kowadce irin gasa ba.
Sannan Kwamitin binciken ya tabbatar Kyaftin din Akurba FC, mai suna Arijide Said Timothy wanda ya jefa kwallaye uku da gangan a ragarsa shi ne kanwa uwar gami wajen janyo ra’ayin sauran ’yan wasan yin coge a wasannin don haka shi ma an dakatar da shi daga buga wasa a kasa har iya tsawon rayuwarsa.
Hukumar NFF ta ce za ta buga hotunan daukacin ’yan kwallon da jami’ansu da alkalan wasan da kuma mataimakansu a jaridu da mujallu da kuma kafofin sadarwa don a hana su canza sheka a ciki da wajen kasa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya