Da Dumi Dumi

Ni ba dan daudu ba ne – Ado Gwanja

Ado Gwanja

Fitaccen mawakin Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finai Ado Gwanja ya ce tsabar yadda ya iya kwaikwayon ’yan daudu ne ya sa ake sa shi a fim din da ya danganci haka.

A wata hira ta musamman da ya yi da sashin Hausa na BBC, Ado Gwanja ya ce duk wanda ya san shi ya san ba ya da wata alaka da ’yan daudu, “Aiki ne za mu yi na fim da ya shafi daudun aka kira ’yan daudun sun fi su 50 amma suka kasa yi.

To sai aka ce bari a gwada dan masana’antar Kannywood din da aka gwada sai aka ga na ma fi su iya kwaikwayon abin sosai, shi ke nan tun daga lokacin sai kuma ake yawan sa ni,” inji shi.

Ado Gwanja, wanda wakokinsa suka shahara a kasar Hausa, haifaffen garin Kano ne, ya ce bai san me ya fi so ba tsakanin waka da yin fim, “Kawai dai na san duka biyun ina son yin su sosai,” inji shi.

Amma mawakin ya fara ne da yin waka, sai dai daga farko da ya ga ba ta karbu ba sai ya hada da fitowa a fina-finai.

ADVERTISEMENT

Yawanci wakokin Ado Gwanja sun fi farin jini a wajen mata saboda yadda yake wasa su, ya kuma ce yana haka ne saboda “Mata aka fi sani da son biki, to idan ba ka wasa su ba wa za ka wasa?” Ya tambaya.

Mawakin mai shekara 29 ya musanta cewa yana sa kalmomin batsa a wakokinsa kamar yadda ake zarginsa da yi, yana mai cewa da Hausa yake wakar ba wani harshe ba, “Kuma a sanina Bahaushe na da fahimta, kuma idan aka dauko wakokina aka zube ba wacce ta shafi batsa,” inji shi.

Ado Gwanja ya fara waka ce shekara 10 da suka wuce, kuma ya ce tsabar ra’ayinta ce ya sa ya fara.

Ya kara da cewa ba koya ya yi ba kuma ba gado ya yi ba, baiwa ce Allah Ya ba shi. “Idan da gado zan yi ai sai dai in yi gadon dafa shayi, don mahaifina fitaccen mai sana’ar shayi ne a Kano,” inji Ado Gwanja.

Kamar yadda yake a bayyane cewa mafi yawan jarumai ko mawaka na cin karo da matsaloli, sai dai Ado Gwanja ya ce duk wanda ya samu kansa a matsala “to shi ya ga dama ya shige ta.”

Kazalika mawakin ya ce a saninsa ba ya da wadansu makiya ko abokan adawa a wannan harka, idan ma akwai su to bai san da su ba. “Kazantar da ba ka gani ba kuma tsabta ce,” inji shi.

Shi dai Ado Gwanja dan asalin Unguwar Kofar Wambai ce a birnin Kano. Kuma mahaifinsa shahararren mai shayi ne a yankinsu.

Ya yi karatu zuwa matakin sakandare, yana mata daya da ’ya daya.-

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya