✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar ta soke takardar shiga kasa tsakaninta da kasashen Afirka

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta soke tsarin karbar takardar shiga kasa a tsakaninta da kasashen Afirka, domin ba wa ’ya nahiyar damar shiga kasar ba tare…

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta soke tsarin karbar takardar shiga kasa a tsakaninta da kasashen Afirka, domin ba wa ’ya nahiyar damar shiga kasar ba tare da wata matsala ba.

Shugaban Kasar Issohou Mahamadou ne ya soke takardar don bai wa dukkan ’yan Afirka damar shiga Nijar kamar ’yan kasar, kamar yadda Ministan Harkokin Waje, Kalla Hankourao ya tabbatar wa Muryar Amurka.

Masu kare hakkin dan Adam sun yaba da wannan tsari, duk da cewa sun ce akwai bukatar a yi taka-tsantsan gudun fada wa tarkon masu tayar da hankali, inda suka ce tabarbarewar tsaron da ake ciki a kasashen Afirka wani abu ne da ya kamata a yi la’akari da shi wajen tafiyar da wannan sabon tsari.