✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Niki Minaj ta soke zuwa yin waka a Saudiyya

Bayan da aka sanar da cewa mawakiyar nan mai shigar tsaraici Nicki Minaj za ta je Saudiyya domin yin waka, kafafen sada zumunta a kasar…

Bayan da aka sanar da cewa mawakiyar nan mai shigar tsaraici Nicki Minaj za ta je Saudiyya domin yin waka, kafafen sada zumunta a kasar da duniyar Musulmi suka barke da ce-ce-ku-ce kan batun.

Sai dai a yayin da al’ummar Musulmi suke sukar shirin zuwan mawakiya Niki Minaj zuwa kasa mafi tsarki a wurun al’ummar Muslumin, sai aka ji mawakiyar ta fitar da sanarwar fasa zuwa kasar ta Saudiyya, inda ta bayyana goyon bayan da take nuna wa mata da kungiyoyin kare ’yancin ’yan luwadi da madigo a matsayin dalilan da za su hana zuwa kasar.

Ana zargin Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado ne yake kawo wadannan sauye-sauye da wadansu suke ganin sun saba wa Musulunci a wani yunkuri da yake yi na bunkasa  bangaren nishadi.

A watan Fabrairun bara ne Saudiyya ta ce za ta ware  Dala biliyan 64 domin bunkasa masana’antunta na nishadi a cikin shekara 10 masu zuwa.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Yawon Bude Ido da Nishadi ta Kasar ya ce an tsara shirya abubuwa 5,000 a bara kawai da suka hada da bikin cashewa na Maroon 5 irin wanda ake gudanarwa a Amurka.

Yarima Mohammed bin Salman ya ayyana kudirinsa na son mayar da Saudiyya “Kasa mai sassaucin ra’ayin addini tare da bude kofa ga dukkan addinai da al’adu da mutanen duniya.”

Domin haka muka kawo muku wasu sauye-sauye da Yariman ya kawo a kasar kamar yadda BBC ya tattaro:

Dage haramci kan silima

A watan Disamban bara, Gwamnatin Saudiyya ta dage haramci kan gidajen silima. Tuni Saudiyyar ta sanar da bayar da damar bude gidajen nuna fina-finai a kasar.

Tarurrukan rawa da waka

Tawagar mawaka ta Cirkue Éloize ce ta farko da ta yi ‘casu’ a watan Janairun bara wanda shi ne karon farko a birnin Dammam na Saudiyya. Bikin na Cirkue du Soleil biki ne irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai. Tuni dai Saudiyya ta fara aikin gina dandalin raye-raye a birnin Riyadh.

Haka kasar ta sanar da cewa za ta gayyaci mawaka irin su Jay Z da Mariah Carey da  taurarin ’yan kwallon kafa irin su Dabid Beckham.

Dage haramcin tuki ga mata

A watan Satumban bara  ma Saudiyya ta sanar da dage haramcin tuki ga mata, kuma tuni aka fara bai wa matan lasisin tuki.

Kafin dage haramcin, Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin yin tuki.

Sai dai duk da wannan ci gaba ga matan Saudiyya, ana zargin hukumomin kasar na bin matakan murkushe wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da ba mata ’yancin tuki.

Bude gidan rawa a Saudiyya

Kazalika, a watan Yunin bana wani gidan rawa na birnin Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna White ya sanar da bude sabon gidan rawar da ya kira “Halal Disco” a Jiddah.

Kafofin watsa labarai na kasar sun tabbatar da bude gidan rawar wanda suka ce tsarinsa ya yi kama sosai da gidan casu na dare da aka sani, sai dai kuma ba za a rika shan barasa a wajen ba.

Shi ma gidan rawar na White ya ce wurin zai yi kama ne da dakin hira ba da mashaya ba.

Bikin ’yancin Saudiyya da ya kawo gwamutsa mata da maza

A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasa don bikin zagayowar ranar ’yancin kan Masarautar Saudiyya.

A watan Satumban shekarar 2017 ne filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh, babban birnin kasar, ya cika makare da daruruwan matan da suka yi dango don cin wannan gajiya.

An ga mata a wasu lokuta ma cakude da maza a kan kujeru suna karkada tutocin Saudiyya albarkacin murnar ranar.

Kallon ’yan kokawan Amurka

A watan Afrilun bara aka bai wa mata da maza damar shiga kallon wasan kokawan Turawan Amurka wato Wrestling.

An gudanar da kokawar na (WWE) a birnin Jiddah, kuma maza da mata ne suka shiga kallon wanda kafar telebijin din kasar ta nuna kai- tsaye.

Maza zalla ne suka fafata a kokawar a Saudiyya yayin da aka haramta damben mata. Sai dai a yayin da mutane ke tsakiyar kallon kokawar sai ga tallar damben mata sanye da kamfai da kananan riguna kamar yadda suka saba.  Hakan ya sa Gwamnatin Saudiyya ta nemi gafara sakamakon kutsen da hoton bidiyon mata ’yan kokawar ya yi.

Shigar mata wajen kallon kwallo

Kamfannin Dillancin Labarai na kasar ne ya sanar da cewa za a rika barin iyalan mutum da suka hada da mata da yara su rika halartar filayen wasanni da ke manyan biranen kasar uku, wato na Riyadh da Jedda da kuma Dammam.

Wannan sabon mataki dai ya fara aiki ne daga farkon bara

Tseren keken mata zalla

A watan Afrilun bara ne kuma aka gudanar da tseren keken mata na farko a kasar, inda suka bai wa mutane da yawa mamaki a kasar.

Kasar Saudiyya dai kasa ce da ta ginu kan addini, kuma wadannan sauye-sauyen suna alamta yadda kasar ke sauyawa cikin sauri zuwa ga rayuwar da ake yi a kasashen Turai.

Sai dai wadannan sauye-sauyen da Yarima Mohammed bin Salman yake bullowa da su a kasar, na sanya mutane cikin rudani da jawo ce-ce-ku-ce ba a Saudiyyar ba har ma a sauran kasashen Musulmin duniya.

Ana kallon Saudiyya a matsayin wata jagora ta addinin Musulunci, shi ya sa duk lokacin da ta bullo da wani abu da ba a saba gani ba yake sanya shakku a zukatan wadansu.