Da Dumi Dumi

Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (3)

A karo na uku GIZAGO (08065576011) ya ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:

A yau za mu yi nazararin baitoci takwas da na tsakuro daga mashahurin waken na ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya?’ Kada mu mance, yau shekarun waken nan 66 da rubutawa. 

Sai mu je ga Malam Yahaya,

Can a Birnin Gwandu, mu kewaya.

 

ADVERTISEMENT

Shaihu Abdullahi hakikatan,

Ya bar mana gadon gaskiya.

 

Ilimi, hikima addini duka,

Da dabarar sarrafa duniya.

 

Muka lalata, muka wargaza,

Ga shi yau sai anai mana dariya.

 

Babu tsuntsu ba tarko duka,

Wallah mun yi hasarar duniya!

 

Jahilci ya ci lakarmu duk,

Ya sa mana sarka har wuya.

 

Ya sa mana ankwa hannuwa,

Ya daure kafarmu da tsarkiya.

 

Bakunanmu ya sa takunkumi,

Ba zalaka sai sharholiya.

 

A cikin wadannan baitoci takwas na sama, Malam Zungur yana ci gaba da bayani da jan hankali da nasiha ga al’ummar Arewa a lokacin. Don haka ya ci gaba da kiran sarakunan Arewa, magada Shehu Usman Dan Fodiyo. Malam ya ambaci sunan Malam Yahaya, Sarkin Gwandu a Jihar Kebbi  a yanzu, sannan ya ambaci sunan kakansa, Shehu Abdullahi Gwandu. Malam ya yi haka ne domin mu waiwayi tarihi, mu duba hanyoyin da wadannan bayin Allah suka bi a tafiyar da rayuwarsu. Idan muka duba tarihi ne za mu tsinci hikima da dabarun da za mu bi mu tsira da duniya.

Malam ya tunatar mana cewa shugabannin nan sun yi aiki da ‘Gaskiya,’ sun yi ‘Ilimi’ kuma sun yi aiki da ilimi, sun yi aiki da ‘Hikima’ wajen tafiyar da lamuransu; haka kuma sun yi ‘Addini’ yadda ya dace, bisa koyarwar Sunnah. Don haka muddin muna son mu tsira kuma mu wanye lafiya, to ya zama wajibi mu dauki gadon magabatanmu na kwarai – mu maida hankali wajen Gaskiya da Ilimi  da Hikima da Addini.

Malam Zungur ya kara mana gargadi, ya nuna mana illar kauce wa turbar magabata da kuma mugun sakamakon da zai same mu idan muka kauce. Tun a zamaninsa, Zungur ya lura da yadda al’ummar Arewa ta fara kauce wa hanyar magabata kuma ta fara girbar sakamakon haka. Misali, mun lalata gadon kwarai, mun wargaza. Mun ki gaskiya, mun ki neman ilimi, mun ki saka hikima a lamuranmu. Sai ga shi mun zama jahilai, mun bari jahilci ya gama cinye mu, mun watsar da gaskiya sai cutar juna, mun watsar da hikima, don haka ba mu da muryar magana.

A sakamakon yin watsi da wadannan turaku na rayuwa, sai muka koma “ba mu ga tsuntsu, ba mu ga tarko, mun yi asarar duniya, sai ga shi ana yi mana dariya.”

Malam, shekara 66 da ta gabata ke nan fa wannan al’amari ya faru, shin yaya Arewa da al’ummarta take a yau? Babu raba daya biyu, mun zama abin dariya a duk duniya saboda mun watsar da gaskiya, mun watsar da addini, mun watsar da hikima, mun watsar da ilimi muka rungumi jahilci da karya da sharholiya. Ya zama dole mu koma baya mu rungumi gaskiya da gaskiya, kamar yadda magabatanmu suka yi.

Wannan ke nan, bari kuma mu sake tsakuro wasu baituka 16 mu gani, kamar yadda suke jere a kasa:

 

Ilimi mai amfani duka,

Inda addininmu ya rataya.

 

In fa addini ya raunana,

Babu alheri nan duniya.

 

Duka cuta Kai ke magani,

Har a san ingantar lafiya.

 

Allah Ka tsare mu da jarraba,

Lahirarmu da rayin duniya.

 

Addu’armu da mu da Sarakuna,

Na Arewa ta zam karbabbiya.

 

Ya Sarki Alhaji Bayero,

Ga ’yan birni da Kanawuya.

Tun Bagauda yana sarar Kano,

Suka fara fataucin dukiya.

 

Hijira ta iske Alwali,

Sai ta karfafa tushen gaskiya.

 

Sabon tsari zan bayyana,

Ban da tajdidi na mutan Gaya.

 

Ai Sulaiman shi ne jagaba,

Kuma Dabo ya bi shi da gaskiya.

 

Ga sarauta, ga ilimi ciki,

Ga adala, shari’ar gaskiya.

 

Sai arnanci ya yi sallama,

Dada har abada ba dawaya.

 

Sarki Abdallah ka taimaka,

Ga Ciroma Sanusi da tarbiya.

 

Ka kiyaye al’ummarka duk,

Don kasarmu ta wanzu Mulukiya.

 

Birni da Fage da Tudun Wada,

Kauyuka, bukkokin tsangaya.

 

Kar ka bar Arna su shige musu,

Don su watsa dafin Jamhuriya.

 

A wadannan baituka, Malam ya ci gaba da warware babban jigon wakensa-Gargadi ga al’ummar Arewa don a guji kauce hanyar gaskiya dangane da abin da ya shafi tsarin mulki da al’amuran rayuwar yau da kullum na al’ummar Arewa a takaice da sauran al’ummar kasa a fadade.

A wancan lokacin, shekara 66 da ta gabata, Malam Zungur ya hango matsalolin da za su baibaye al’ummar Arewa, musamman sakamakon bijiro da Tsarin Mulkin Nasara na Jamhuriya da ake kokarin kakaba wa Najeriya, wanda haka ke nufin Arewa za ta yi rashin ingantaccen Tsarin Mulkin Mulukiya, wanda ya ta’allaka da addini, adalci, gaskiya da zumunci.

A baitocin nan 16, Malam Zungur ya bijiro da wasu tubalan rayuwa da yake gargadin Sarakunan Arewa da al’umma su kula da su, domin kauce wa fadawa cikin hallaka.

Tubalan da za mu nazarta a wadannan baitoci 16 na Malam sun hada da: Ilimi da Tarihi da Addini da Arnanci da Kasuwanci. Kowane tubali, yana dauke da bayani mai kima da zai taimaka ko ya nakasa al’umma.

Ilimi: Malam ya bayyana mana cewa ya zama dole al’ummar Arewa ta maida hankali kan ilimi, ilimi mai amfani wanda bai kauce wa tsarin addini ba. Babu shakka babu abin da ya kai girman ilimi wajen samun kowace nasarar rayuwa.

Allah (SWT) a Alkur’aninSa, ayoyin farko da Ya saukar, suna umarni ne a nemi ilimi. Mu duba Suratul Alak (96:1-5), Allah Yana cewa: “Karanta da sunan Ubangijinka Mahalicci. Wanda Ya halitta mutum daga gudan jini. Karanta kuma Ubangijika Shi ne Mafi girma. Wanda Ya koya (a yi rubutu) da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.”

Haka Manzon Allah (SAW) ya farlanta wa al’umma maza da mata su tashi su nemi ilimi komai nisa, koda zuwa kasar China ne. Don haka Malam Zungur ya jaddada muhimmancin ilimi a baitocin nan.

Tarihi: Malam ya nemi al’umma su waiwayi tarihin adalan Sarakunan Arewa da suka shimfida mulkin adalci da gaskiya, mai ruhin addini. Bisa kan haka, ya ba da misali da Kano, inda ya ambaci sunayen Sarakunan Kano Abdullahi Bayero da magabatansa Sarki Sulaiman da Sarki Dabo. Zungur ya nuna cewa wajibi ne masu mulki su yi koyi da magabatan kwarai, a rike addini da ilimi da adalci da gaskiya, idan ba haka ba babu alheri a rayuwarmu da za mu gani.

Addini: Malam ya gargade mu da lallai mu yi riko da addini. Sarakunanmu kada su yarda da tsarin arnanci, wanda ake son a dibiya shi ga Arewa ta hanyar Tsarin Jamhuriya.

Kasuwanci: Malam ya sanar da mu muhimmancin kasuwanci, wanda ya ambata da fatauci. Ya ba da misali da al’ummar Kano, cewa tun Bagauda na gina kasar suka shahara da kasuwanci. Ke nan Zungur na nufin kada mu kasance cima-zaune, mu yi sana’a domin kauce takaici da kaskanci.

’Yan uwa, wannan shi ne kadan da hankalina ya nakalto daga wadannan mashahuran baitoci na Malam Zungur. Abin tambaya a nan shi ne, shin yaya al’ummarmu take a yau, idan muka dubi tsokacin Malam Sa’adu Zungur?

Za mu ci gaba

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya