✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Noman auduga zai iya kawar da talauci a Najeriya’

Daraktar Cibiyar Binciken Aikin Gona da Samar da Iri (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Umar Abubakar, ya bayyana noman auduga…

Daraktar Cibiyar Binciken Aikin Gona da Samar da Iri (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Umar Abubakar, ya bayyana noman auduga a matsayin abin da zai kawar da talauci a Najeriya.

Farfesa Ibrahim Umar ya bayyana haka ne a lokacin taron manoman auduga na jihohi takwas na Arewa a Cibiyar IAR da ke Zariya.

Farfesa Ibrahim Umar, ya ce  a baya kimanin kashi 55 na kudin shiga da kasar nan take samu a cikin gida yana fitowa ne daga noman auduga. Ya bayyana haka ne lokacin taron shekara-shekara na bana kan bunkasa noman auduga da aka gudanar a Cibiyar IAR.

Farfesa Ibrahim Abubakar, ya ce a farkon shekarun 1980 a kasar nan akwai kamfanoni da ke gurzar auduga akalla 51, wanda hakan ya samar wa matasa kimanin dubu 700 ayyukan yi a kasar nan.

Ya yaba wa Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba da sauran masu ruwa-da- tsaki bisa kokarinsu na ganin an bunkasa noman auduga a kasar nan.

A kasidar da ya gabatar mai taken: ‘Kawar da talauci ta hanyar noman auduga’, wani mai harkar masaku da ke Kano, Alhaji Sa’idu Dattijo Adahama, ya ce kashi 90 na audugar al’ada da mata ke amfani da ita da wadda asibitoci ke amfani da su ba wanda ake shukawa a Najeriya ba ne.

Alhaji Sa’idu Dattijo Adahama
Alhaji Sa’idu Dattijo Adahama

Ya yi nuni da cewa, ana matukar samun kudi da dimbin amfani a noman auduga, amma abin takaici sai gwamnatocin da suka gabata suka yi watsi da dangaren.

Dattijo Adahama, ya kara da cewa a Jihar Kano kawai, akwai mata sama da miliyan biyar da ke amfani da audugar al’ada duk wata baya ga asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya da su ma suke amfani da audugar.

Ya ce idan aka lissafa wadannan mata miliyan biyar suna sayen audugar ce koda a kan Naira daya, za a samu Naira miliyan 500 ke nan duk wata wajen sayen audugar da matan ke amfani da ita.

Ya ce sauran dangarori da ke yin soso, ko singileti da maza ke amfani da ita kullum da wadanda ke yin shimin mata su ma da auduga suke saka su. Don haka noman auduga na iya kawar da talauci a Najeriya.