✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noman zamani: Darussan da Najeriya za ta koya daga Brazil

A yau kasar Brazil ce kan gaba a fagen arzikin noma da samar da yawan amfanin gona a duniya. Haka kuma kasa ce mai arzikin…

A yau kasar Brazil ce kan gaba a fagen arzikin noma da samar da yawan amfanin gona a duniya. Haka kuma kasa ce mai arzikin man fetir, dalilin ma da masana ke kamata yanayin kasar da Najeriya. Brazil ta na da yawan al’umma kimanin miliyan 207 da dubu 800. 

Koda yake Brazil ta samu koma baya a harkokin noma tsawon lokaci, amma tun bayan dorewar mulkin dimokuradiyya a kasar, ta fara maida hankali wajen inganta harkokin nomanta, lamarin da cikin kankanin lokaci ya samar da ayyukan yi ga miliyoyin al’ummar kasar, inda fiye da kashi daya bisa uku na adadin masu aiki a kasar daga noma ne. 

Ba kawai Brazil ta dogara da kanta ne ta fuskar abinci ba, ita ce kan gaba cikin kasashe mafi fitar da kayan amfanin gona a duniya. Brazil ta fi kowace kasa fitar da rake da koko da waken soya da kofi da kuma lemu. Kayan noma su ne kashi 35 cikin 100 na abinda kasar ke fitarwa zuwa kasashen ketare. Haka kuma a bangaren kiwo, ita ce kan gaba wajen fitar da jan nama da kaji a duniya. 

kasar Brazil ta zarta sa’a ne bisa aniyar shugabanninta, inda suka kafa manyan gidajen gona, yayin da kuma su ka karfafa kananan gonaki da bincike da bude kasuwanci a faifai sannan da kuma amfani da dabarun noma na zamani. Ana kallon manomansu a mataki na duniya, ba wai cikin kasarsu kadai ba. 

Brazil ta na da murabba’in kasar noma kimanin hekta miliyan 76 da dubu 700. Sannan alkaluma sun bayyana cewa kasar Brazil ta na shanu fiye da miliyan 219. Haka zalika Brazil ta na fiye da murabba’in hekta miliyan 23 da a ke noma waken soya kadai akanta. Masara ta na da hekta miliyan 12 sai kuma rake na da hekta miliyan 7, yayin da shinkafa ke da hekta miliyan 2.5.  

kasar Malesiya, wacce ta fara samun irin kwakwa daga Najeriya a shekarun 1960, a yau ta zama abar misali a duniya a fagen noman kwakwa. Domin ta na noma fiye da hekta miliyan 4 na kwakwa, lamarin da ya bata damar zama kasa ta biyu a duniya bayan da kasar  Indonisiya ta zarta ta wajen fitar da kwakwa a duniya. 

Da wannan ne masana ke ganin Najeriya ta na da irin wannan dama a fagen noma da kiwo tamkar wadannan kasashe uku. Akwai ma lokacin da Najeriyar ta taba kasancewa kasa mafi fitar da gyada da manja da roba da koko a fadin duniya baki daya. Bugu da kari, a wancan lokaci Najeriya na cikin kasashen da ke kan gaba wajen fitar da auduga da karo da fata da kuma a duniya.