✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya dakatar da nadin kwamishinoni biyu na Hukumar ICPC

Zargin cin hanci ya talista wa Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo dakatar da sabbin nade-naden da ya yi wa mutum biyu a Hukumar Yaqi da…

Zargin cin hanci ya talista wa Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo dakatar da sabbin nade-naden da ya yi wa mutum biyu a Hukumar Yaqi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC.
Wani babban jami’in gwamnati wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda wasu dalilai  shi ne ya tsaigunta wa wakilin Aminiya a fadar shugaban kasa lamarin ta saqon wayar salula.
Jami’in gwamnatin ya ce tuni Osinbajo ya dakatar da nadin da ya yi wa Mista Sa’ad Alanamu da Mis. Maimuna Aliyu a ranar Talatar da ta gabata.
Tun ranar Juma’ar da ta gabata Cibiyar Kasa da Kasa da ke Yada Rahotannin Bincike ta (ICIR) ta ruwaito cewa tuni Hukumar ICPC ta yi nisa a binciken da take yi wa Maimuna Aliyu,Tsohuwar Shugabar Bankin Ajiya da bayar da Bashi na Aso Savings kan zargin satar kudi da karkatar da kudin jama’a tun kafin Osinbajo ya nada ta a mukamin memba a hukumar gudanarwar Hukumar ICPC.
Rahotanni sun nuna cewa ana binciken Mista Sa’adu Alanamu kan zargin cin hanci a lokacin da yake Shugaban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara.
“Daukacin kwamishinoni biyu da aka nada na Hukumar ICPC wadanda aka bayar da rahoton ana bincikarsu za su sauka daga kan mukamansu kuma ba za su kansace membobin Hukumar ba”. Inji Jami’in Gwamnatin