✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ozil ya aiko wa yaro dan Kenya takalmin kwallo

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya aiko wa wani yaro dan kasar Kenya kyautar takalmin kwallo da rigunan Arsenal da ke dauke da sunansa. Lawrence…

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya aiko wa wani yaro dan kasar Kenya kyautar takalmin kwallo da rigunan Arsenal da ke dauke da sunansa.

Lawrence Masira mai shekara 12 dan kasar Kenya ne mai goyon bayan kungiyar Arsenal da Ozil.

Yaron dan kabilar Maasai ya rubuta sunan Mesut Ozil ne a bayan wata rigar kwallo kamar ta Arsenal da mahaifiyarsa ta saya ma sa.

Hoton yaron da aka dauka aka wallafa a Intanet ne ya ja hankali har Ozil ya gani.

Yaron ya ce Ozil ne gwaninsa a Arsenal saboda yadda yake taka leda da kuma yadda yake taimaka wa Arsenal din take cin kwallaye.

An yi ta yada hoton yaron sanye da rigar kwallon yana kiwon shanu a Tiwita wanda wani dan jarida ya dauka.

Dan jaridar ne ya fara wallafa hoton kuma ya alakanta hoton zuwa ga Ozil don ya taimaka wa yaron.

Nan take Ozil ya aiko wa dan jaridar da sako cewa ya ji dadi kuma yana son taimaka wa yaron.

Ozil ya aiko wa yaron da takalmin kwallo da rigunan Arsenal dauke da sunansa ta hanyar dan jaridar mai suna Eric.

Yaron ya ce ya ji dadi kuma yana fatan wata rana zai yi ido biyu da Ozil.