✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ozil ya dauki nauyin yi wa yara dubu tiyata a Siriya

Shahararren dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila kuma dan asalin Jamus Mesut Ozil ya dauki nauyin yi wa wadansu yara kimanin dubu 1…

Shahararren dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila kuma dan asalin Jamus Mesut Ozil ya dauki nauyin yi wa wadansu yara kimanin dubu 1 tiyata a kasar Siriya.

Dan kwallon ya ce ya dauki nauyin ne saboda murnar angwancewa da ya yi da amaryarsa Amine a karshen makon jiya inda dubban ’yan uwa da abokan arziki suka halarta.

Ozil ya nuna cewa taimakon ba a nan kawai zai tsaya ba, yana fatan ya karade sassan duniya wajen ci gaba da bayar da irin wannan taimako.

Ozil ya shawarci abokansa musamman masu hali su yi koyi da shi wajen tallafa wa mabukata a ko’ina suke a duniya.

Ozil ya dade da hada kai da wata kungiya da ke taimakon al’umma a duniya mai suna BigShoe.

Kungiya ce da ta tattaro kwararrun likitoci daga Jamus da Switzerland inda suke bi kasashen duniya suna yi wa mabukata tiyata kyauta.

“A matsayina na shahararren dan kwallon kafa kuma wanda yake da hali, ina kira ga masu hannu da shuni su rika taimaka wa talakawa a duk inda suke,” inji Ozil.

Bayan da aka gama gasar cin Kofin Duniya a bara a Rasha ne suka Ozil ya kulla yarjejeniyar taimakon al’umma a sassan duniya da kungiyar BigShoe inda kawo yanzu suka gudanar da taimakon jinkai a Brazil da Afirka da kuma Rasha.

Dubban yara ne suke fama da lalurori daban-daban a Syria musamman a wannan lokaci da yaki ya kacaccala kasar.