Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

PDP za ta je kotu kan sakamakon zaben Gwamnan Kano

Injiniya Abba Kabir Yusuf
Injiniya Abba Kabir Yusuf

Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ta yi watsi da sakamakon zaben raba gardama na Gwamnan Jihar da aka yi ranar Asabar da ta gabata tare da bayyana zaben a matsayin fashi da rana-tsaka.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a miliyan daya da dubu 33 da 695 inda abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir ya samu kuri’a miliyan daya da dubu 24 da 713.

ADVERTISEMENT

Wata takarda da Kakakin dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Jam’iyyar ta PDP ta ce abin da ya faru a zaben cike gurbi ba komai ba ne illa kwace tare da daure wa harkar daba gindi a harkar zabe a jihar.

A cewar Jam’iyyar PDP duk da cewa ta rubuta wa Hukumar INEC kan ta soke gudanar da zaben lura da abin da yake faruwa a lokacin zaben amma hukumar ta yi kunnen uwar shegu da bukatar jam’iyyar wanda hakan yake nuni da rashin adalci daga hukumar.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, jam’iyyar ta yi mamakin yadda Rundunar ’Yan sanda ta bayyana zaben a matsayin wanda aka aiwatar da shi lafiya ta bakin Mataimakin Sufeto Janar, Anthony Michel wanda aka tura jihar aka ajiye Kwamishinan ’yan sandan jihar a gefe.

Takardar ta bayyana takaicin cewa duk da irin harkallar da ta faru a yayin zaben Hukumar INEC ta runtse idanunta a kan dukan kura-kuran da aka tafka a wajen gudanar da zaben har ta kai ga bayyana sakamakon zaben.

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga magoya bayanta su zauna lafiya kuma jam’iyyar tana tattaunawa da lauyoyinta tare da hada hujjoji don daukar matakin shari’a’ a kan lamarin. “Mun yanke shawarar daukar matakin shari’a kasancewar muna da hujjoji da muke da su kuma insha Allah za mu karbo hakkin al’ummar Jihar Kano da aka kwace ta karfin tsiya,” inji sanarwar.