✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qaramin jirgin ruwa mai tashi sama

An ga karamin jirgin ruwa mai tashi sama a gabar kogin Yazhou, da ke birnin Sanya da ke Kudancin kasar Sin. Kamfanin hada-hadar sufuri na…

An ga karamin jirgin ruwa mai tashi sama a gabar kogin Yazhou, da ke birnin Sanya da ke Kudancin kasar Sin.

Kamfanin hada-hadar sufuri na Kudancin kasar Sin ya kirkiro shi don yin kai-kawo daga birnin Sanya zuwa tsibirrin Yongding da ke tekun Kudancin kasar Sin. Jirgin ruwan mai tashi sama yana cin kilomita 160 zuwa210 a kowace sa’a guda, a kalla an kiyasta gudunsa ya nunka na karamin jirgin ruwa sau uku zuwa biyar. Jirgin na tashi a kan ruwan teku kamar yadda jaridar People’s Daily China ta ruwaito.