✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rabe-raben tsaga a al’adar Hausawa

Tsaga wata alama ce da kabilu daban-daban kan yi ciki har da  Hausawa da  aska a fuska ko a jiki, saboda bambanta wata kabila da…

Tsaga wata alama ce da kabilu daban-daban kan yi ciki har da  Hausawa da  aska a fuska ko a jiki, saboda bambanta wata kabila da wata, ko dangi da  dangi, ko  don rikon al’ada ko don kwalliya ko don kawar da wata cuta. Malam Yusuf Maigidan Sama, kwararre kuma marubuci a fannin adabi ya yi cikkaken bayani a kan ire-iren tsaga da Hausawa kan yi.

An kasa tsagar gargajiya zuwa kashi uku kamar haka:

  1. Tsagar magani
  2. Tsagar gado
  3. Tsagar ado ko kwalliya

Zai yi kyau a kawo matsakaicin bayani kan sana’ar wanzanci, saboda dangantakar da  ke akwai, tare da  alaka a tsakanin sana’ar da  al’adar tsaga ta gargajiya.

Wanzanci

Wanzanci sana’a ce ta yin amfani da aska domin gusar da gashi, ko yin kaciya, ko yin kaho ko kuma tsaga domin rikon al’ada. Wanzanci sana’a ce gadajjiya a al’adar Hausawa. Wanzamai na matukar alfahari da wannan sana’a saboda muhimmancin da take da shi a wajensu. Wannan shi ya sa suka kebantu da wasu tsage-tsage, ko don ado ko don magani wajen kawar da wata cuta da ta darsu a jikin mutum.

Tsagar magani

Ita ce wadda akan yi domin maganin wata cuta a jikin mutum. Galibi irin wannan cuta takan danganci jini ne, ko abin da ya shafi ciwo na cikin jiki. Tsagar magani tana da yawa kuma takan danganci yanayi na irin cutar da ta samu mutum. Hausawa sun yarda kuma sun amince cewa, mataccen jini ne kan sabbaba mafiya yawan cututtukan da ke damun mutum a jiki. Watakila wannan ce ta sa Hausawa suka fi mai da hankali wajen maganin da ya shafi huda jiki ko tsagawa yayin da wata cuta ta same su. Misalin irin wannan shi ne, tsagar zarar-danshi ko fashin goshi don maganin tafiyar ruwa da tsagar kanne (tsaga a karkashin ido) da kaho da balli-balli da sauransu. Ga dai bayani kan wadannan tsaga:

Tsagar balli-balli

Tsaga ce ta gajeriya siririya. Takan zama uku-uku ko hudu-hudu a bisa dorin gado biyu. Sai dai an fi yin ta a barin hagu na karkashin nono. Shi balli-balli, wani ciwo ne da yara suke yi a kirjinsu wanda yakan hana su jan numfashi sosai. Idan an kai wa wanzami zai saka hannunsa a kan kirjin yaro ya ji wurin da ya fi harbawa, sai ya saka aska ya tsatssaga wurin, sannan jinin ya zuba, yaro kuma ya samu lafiya. Hakaana tsagar balli-balli don gusar da cutar ‘asma’ da kuma ‘tasa’ wadanda a zamanin da yara ne suka fi yin su. Cututtukan sukan kama su ne a shekaru bakwai zuwa kasa.

Tsagar zarar-danshi

Tsaga ce ta gargajiya a kan goshi mai kama da fashin goshi wadda ake yi wa yaron da cutar zarar-danshi ta kama shi, Yanayin cutar shi ne, a ga yaro yana suma kuma idanuwansa a kakkafe. Irin wannan cuta ta fi kama yaran da ba su wuce shekara biyu a duniya ba.

Tsagar kanne

Tsaga ce gajeriya mai kama da bille sai dai ba ta sauko daidai wajen da ake yin billen ba. Domin akan yi ta ce daf da karkashin ido. Manufar wamnan tsaga ita ce, saukaka radadin ciwon ido wanda wannan gurbataccen jini kan iya haifarwa.

Tsagar jiri (datsa)

Tsaga ce da ake yi a saman gira. Takan kasance guda bibbiyu ko fiye a kan kowace gira, manufar wannan ita ce, yin maganin cutar jiri, wato mutum ya rika jin kansa dundurum ko kuma hajijiya ta dame shi. Wani lokaci idan mutum yana fama da ciwon ido ko dindimi akan yi masa tsaga uku-uku a saman gira, domin ya samu lafiya.

Kaho

Wanzami yakan yanka kahon saniya ya mayar da shi kamar misalin danni guda da kari (tsawon babban dan yatsa da karin gaba daya) sai ya kankare shi ciki da waje, ya gyara bakin yadda zai dakushe kaifin. In ya gama sai ya huda kansa, ya yi ’yar kofa siririya a sama, Lokacin da wanzami zai yi kahon yakan dubi mutumin da za a yi wa ko yana da isasshiyar lafiyar da zai iya daukar kaho fiye da daya a lokaci guda ko kuwa? Daga nan sai ya yanke shawarar adadin da zai yi masa, gwargwadon karfin jininsa.

Bayan haka, sai wanzamin ya kafa kaho a daidai inda cutar take a jikin majinyacin, ya rika zuko iska yana jawo fatar wajen da zai yi kahon. Idan kahon ya tsaya daidai sai wanzamin ya like kofar da jijiya ko danko. Idan an kafa wa mutum kaho, akan bari sai ya yi kamar minti goma a jikinsa don mataccen jini ya taru wuri guda, sai a cire a tsattsaga kan wurin da ya dago saboda taruwar jinin. Sannan a mayar da kahon a sake zukowa a like samansa shi ma za a bar shi kamar minti goma, sannan a cire.

To a wannan lokaci ne za a ga mataccen jinin ya taru a cikin wannan kaho, sai a juye a kasa a kuma mayar da kahon. Haka za a yi ta yi har iyakacin yadda ake bukata. Wadansu wanzaman sukan shafa magani bayan sun kare. Wadansu kuwa ba sa saka komai, matukar dai sun gusar da wannan mataccen jini.