Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Rabiu Usman Baba ya rasu

Mutuwa rigace wacce ba ta fita.

Da sanyin safiyar  yau Alhamis muka samu rahoton cewa Allah Ya yi wa fitaccen sha’irin nan, Sheriff Rabiu Usman Baba rasuwa.

ADVERTISEMENT

Wanda aka gudanar da jan’izarsa a gidansa da ke kofa ta biyu watau ‘’Second Gate’’ da ke unguwar Janbulo cikin Birnin Kano.

Kafin rasuwar tasa, Rabiu Usman Baba ya shahara wajen rera wakokin yabo ga Manzon Allah (SAW) da Iyalansa, inda har ya ciri tuta kuma ya zamo shugaban kungiyar mawakan Manzon Allah (SAW), wato Shu’ara’ul Islam ta Najeriya gaba daya.

ADVERTISEMENT

Zuwa yanzu dai jama’a da dama na ci gaba da bayyana alhininsu game da mutuwar babban sha’irin, tare da jimamin rashinsa, musamman duba da yadda wakokinsa suka yi tasiri a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyyah da Qadiriyya. Wasu daga cikin fitattun wakokin Rabiu Usman Baba sun hada da Tauhidi; Babu tantama, Tsumagiya, sha yabo, majalisi, wakar Sadiya, zumunci, tambaya, sharifai, Fadima, Garkuwa, Batijaniya, Bakadiriya, Fiyayya, Sayyadil Wara da Zuma.

Da fatan Allah Ya jikansa da gafara, da dukkanin Musulman da suka rigamu gidan gaskiya, Amin.