✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahin kyan hanya ke jawo mana fashi a Zamfara – Adamu Musa

Wani dan asalin Jihar Zamfara mazaunin Legas Malam Adamu Musa ya ce mutanen Jihar Zamfara na cikin muwaycin hali saboda rashin kyan hanya. Malam Adamu…

Wani dan asalin Jihar Zamfara mazaunin Legas Malam Adamu Musa ya ce mutanen Jihar Zamfara na cikin muwaycin hali saboda rashin kyan hanya.

Malam Adamu Musa dan asalin kauyen Gazura da ke karamar Hukumar Gumi a Jihar Zamfara ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Legas, inda ya ce, “Gaskiya muna cikin tsaka mai wuya saboda rashin kyan babbar hanyar da ta tashi daga garin Zaru zuwa Kwantagora zuwa garin Zamfara. ’Yan fashi na takura mana suna cin karansu ba babbaka. Saboda akwai wata gada da ake kira gadar Liyoji da ta karye kuma har yanzu gwamnati ba ta gyara ba. barayi na amfani da wannan dama suna yi wa mutane fashi.”
Ya ce a yanzu haka manyan motoci sun daina bin hanyar sai dai su zagaya ta Yawuri. “A tsakanin daki-Takwas zuwa Zuru mutane da ’yan kasuwa suna yin asarar dukiya da rayuka masu yawa sakamakon barnar da ’yan fashi suke yi musu,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar su hada karfi su gyara hanyoyin da suka lalace don amfanin mutanen yankin.