Da Dumi Dumi

Ranar Idi: Takaddamar ganin wata a bana

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar
Al’ummar Musulmi a fadin Najeriya sun shiga halin rudani a kan ranar da za a yi Idin karamar salla a kasar, bayan samun rahotannin ganin wata a wasu yankunan jihohin Yobe da Bauchi da Kebbi da kuma birnin Zaria da ke jihar Kaduna.
Labarin ganin watan dai ya zo ne sa’o’i kadan bayan sanarwar da Sarkin Musulmi kuma shugaban Jama’atul Nasril Islam, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi, cewa ba a ga watan ba.
Ganin wata dai shi ne ya ke tabbatar da karewar watan Ramadan wanda a cikin shi al’ummar Musulmai ke gudanar da azumi da kuma farawar watan Shawwal wanda a cikin shi ake gudanar da karamar sallah.
Sanarwar ta Sarkin Musulmi ta zo ne bayan da kasar Saudiyya ma ta bayyana cewa ba a ga watan ba kuma ta bayyana cewa za a cike azumi 30.
A wani bangaren kuma, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda jagora ne na Darikar Tijjaniya a Najeriya, ya bayyana cewa zai jagoranci jama’arsa su gudanar da sallar a ranar Asabar, sakamakon  samun rahoton ganin watan a wani yankin a jihar Bauchi da garin Zaria.
Shehin Malamin ya bayyana haka ne a wani sakon murya da ya aike wa mabiyansa inda ya yi zargin cewa an mika rahoton ganin watan ga sarkin Musulmi amma ya yi watsi da shi, saboda “rahoton ganin watan da aka mika mishi bai zo cikin lokaci ba”.
Takaddama a garin Zaria
A garin Zaria dake jihar Kaduna ma an samu wata takaddamar, inda Babban Limamin Masarautar Zazzau, Dalhatu Kasimu, ya sanar da cewa an ga wata.
Jim kadan bayan sanar da hakan a shafinsa na Facebook, Wazirin Masarautar, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, ya fito ya yi watsi da sanarwar, ya kuma  jaddada kudurin su na biyayya ga umarnin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.
A wata sanarwa da ya fitar ya ce, “Kwamitin ganin wata na Masarautar Zazzau bisa jarogancin Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim  Muhammad Aminu na sanar da jama’ar kasar Zazzau da dukkan Musulmi cewa kwamitin ya ba da umurnin a ajiye azumin watan Ramalan gobe Asabar 23 ga watan Mayu, 2020”.
Sakon ya kara da cewa mai martaba  Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, yana kira ga jama’a da su bi umarnin Mai Alfarma Sarkin Musulmi saboda a cewarsa shi ne ya ke da alhakin sanar da ganin watan.
“Haka kuma jawabin da Limamin Zazzau, Malam Dalhatu Kasimu Imam, ya bayar ba da umurnin Mai Martaba Sarkin Zazzau da Majalisar sa ba ne”, in ji sanarwar.
Zanga-zanga a fadar Sarki Musulmi
A ranar Asabar da safe ne kuma wani hoton bidiyo, wanda yake nuna daruruwan jama’a da suka yi tururuwa zuwa Fadar Sarkin Musulmi suna zanga-zanga,  ya yadu a shafukan sada zumunta wanda masu yada shi suka danganta da halin da ake ciki.
A martanin da Fadar Sarkin Musulmin ta mayar a kan bidiyon, jami’in hulda da jama’a a Majalisar Sarkin Musulmi Aminu Haliru Gidadawa ya ce wannan bidiyon ba na yanzu ba ne, domin an dade da dauka tun a wani zabe ne da aka yi wasu suka yi haka masu cewa a wannan Sallar ne aka yi ‘ba gaskiya ba ne’.
‘Ba mu da masaniyar sanarwar kwamitin ganin wata a facebook’
Bugu da kari shafin Facebook na kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara a kan harkokin ganin wata ya fitar da bayani inda yake kira ga duk wanda yake da labarin ganin watan da ya gabatar da kansa saboda sake duba hukuncin da suka yanke a jiyan.
Majalisar Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ta ce ba ta da wata masaniya kan takardar da ke yawo a kafofin sada zumunta na zamani dake nuna babban kwamitin ganin wata na kasa ya ba da sanarwar cewa duk wani mutum da ya ga jinjirin watan shawwal ya zo suna nemansa domin neman karin bayani a wurinsa.
Kwamitin ganin wata a Abuja
Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin ganin wata a Majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid a zantawarsa da wakilin Aminiya  a wayar tarho ya ce “Akwai babban kwamitin ganin wata na kasa dake Abuja da muke aiki tare da su, amma ko sun fitar da wannan bayani ko ba su fitar ba ban sani ba, ban ga wannan rubutun ba”.
Farfesa ya ce ku tuntube su in sun ce sun sanar da mu shi ke nan.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya