Rayuwa da ilimi mai amfani ta fi rayuwa da kudin da ba za a amfana ba:

64.  Rayuwa da ilimi mai amfani ta fi rayuwa da kudi mai amfani balle wanda ba mai amfani ba.

65. Rayuwa da ilimi mai amfani da hankali da lafiya da numfasawa, mai nagarta ga abinci da sha da sutura da wurin kwana natsatse kudi ba zai ba ka su ba.

66. Rayuwa da kudi komai yawansu in ba dayan wadannan balle wasunsu, kudin ba su yin dadi, ko da ba na bashi ba.

67. Rayuwar mutum kullum mai son yana tare da rai da lafiya da zama lafiya ne da hankalinsa kwance ba a tayar masa ba.

68. Rayuwa na tare da hankali ne da biyan bukata in an samu biyan bukatarsu, sai su kwanta ba barci ne suke yi ba.

ADVERTISEMENT

69. Rayuwa in ta tashi tsaye, hankali kuma sai ya tashi, fitinar da ke barci su tashe ta, wadda ba a so, farkawarta ba.

70. Rayuwar mai bidar ilimi ba irin ta mai neman kudi take ba, ta salama ce da mika kudi dayansu ba zai ba da ilimi ba.

71. Rayuwar neman kudi da kudi ne ko da karfi, sannan ga halal da haram a cikinta; shi kuwa na ilimi ba a kama ka in ba da aiki ba.

72. Rayuwa da bidar ilimi ko ba ka ganewa akwai riba, ko a kan masu ganewa in ba su aiki da shi, ba su fi ka komai ba.

73.  Rayuwa da bidar ilimi ta fi ta neman kudi don ci da tara ta, ba taimakon na kusa balle wadanda ba kusa ba.

74. Rayuwa don a ce maka mai kudi matsala ce in dai ba don wadancan bukatun da aka ambata ba, da taimakon gajiyayyu masu neman halal da wadanda ba za su iya neman wa kansu ba.

 

Za a iya samun Malam Mahmud Sabo Wushishi ta: 08055736329,

08034358678

Share