Real Madrid ta fitar da rigar wasanta na kakar wasa mai zuwa

A ranar Litinin da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fitar da sabuwar rigar da ’yan wasansa za su yi amfani da ita a kakar wasa mai zuwa.
Sabuwar rigar mai dauke da tallar Kamfanin Jirgin Sman Fly Emirates ta yi daidai da wacce kulob din Arsenal da ke Ingila da na Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa da kuma na AC Milan da ke Italiya suke amfani da su a gaban rigunan a matsayin talla.
Shi dai kamfanin jirgin saman Fly Emirates ya kulla yarjejeniyar yin talla ne a tsakaninsa da kulob din Madrid a farkon kakar wasa ta bana.
An yi bikin kulla yarjejeniyar ce a filin wasa na Madrid watau Santiago Bernebeu inda aka samu halarcin shugaban kulob din Florentina Perez da wasu manyan daraktoci da kuma daukacin ’yan wasan kulob din.  A bangaren kamfanin kuma shugaban kamfanin Sheikh Ahmed bin Saeed Al Maktorum, ne ya jagoranci tawagarsa don wajen kulla yarjejeniyar.
A da kulob din Madrid yana yi wa kamfanin nishadantarwa na ‘Bwin” talla ne a gaban rigarsa amma yanzu ya canza akalarsa zuwa “Fly Emirates” a kakar wasa mai zuwa.