Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Rikici tsakanin Fulani da mafarauta ya ci mutum 37 a Mali

Fulani 37 ne suka rasu sakamakon wani hari da mafarautan Dozos suka kai musu a yankin Mopti da ke kasar Mali bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu.

Wata sanarwa da Gwamnatin Mali ta fitar, ta nuna cewa da safiyar Talatar da ta gabata ce mafafarauta na Dozos suka kai wani kazamin hari a kauyen Koulogon da ke kusa da garin Bankass.

ADVERTISEMENT

Mafarautan  wadanda suka je kauyen a kan babura sun bude wa Fulani wuta inda mutum 37 da suka hada da mata da yara kanana suka rasa rayukansu.

Fulani makiyaya da ke rayuwa a tsakiyar kasar Mali na fuskantar hare-hare a ’yan shekarun da suka gabata.

ADVERTISEMENT