✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin hijabi: Gwamnatin Legas ta nemi sasantawa da al’ummar musulmi

Gwamnatin jihar Legas ta zabi  sasantawa a wajen kotu kan rikicin da take yi da al’ummar musulmin jihar dangane da ’yancin sanya hijabi ga dalibai…

Gwamnatin jihar Legas ta zabi  sasantawa a wajen kotu kan rikicin da take yi da al’ummar musulmin jihar dangane da ’yancin sanya hijabi ga dalibai mata da ke karatu a makarantun firamare da na sakandaren jihar.
A zaman da babbar kotun jihar da ke yankin Ikeja ta yi karkashin mai shari’a Olubunmi Oyewole, lauyan gwamnatin jihar Samuel Muniru Ajanaku ya shaida wa kotun cewa gwamnatin jihar ta dakatar da kalubalantar bangaren da ya shigar da karar ne saboda imanin da ta yi cewa lamari ne da za a iya sasantawa a wajen kotu.
Da yake mayar da martani lauyan wadanda suka shigar da kara, wato al’ummar musulmin jihar, Taiwo Hasan Fajimite ya ce sun yi bakin ciki da ya kasance gwamnati ba ta shigar da takardunta ba, sai yanzu, amma ya dage a kan cewa al’ummar musulmi za su duba hujjojin da gwamnatin ta ba su don ganin ko sun dace da bukatun al’ummar musulmin jihar.
Daga nan sai mai shari’a Oyewole ya bukaci bangarorin biyu su tattauna da juna  sannan daga bisani su sanar da kotun sakamakon tattaunawar a zaman da kotun za ta yi kan batun a ranar 10 da watan Julin shekarar da muke ciki.
Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun lauyan al’ummar musulmi Fajimite ya ce amincewar da al’ummar musulmi suka yi da bukatar gwamnatin na sasantawa a wajen kotu ba yana nufin za su janye shari’ar ba ne.
“Bayan da muka shigar da takardunmu gaban alkalin kotun mai shari’a Olubunmi Oyewole, sai muka fahimci gwamnatin jihar ba ta shigar da nata takardun ba, sai da safe, daya daga cikin lauyoyinsu mai suna Barister Ajenifuja ya shaida mana cewa ba su shigar da takardun ba saboda sun yi imanin cewa lamari ne da za a iya sasantawa a wajen kotu. Sai muka ce tun da mun san  doka ta ba da damar a sasanta a wajen kotu, sai muka ce to bari mu ga yadda za ta kaya. Amma mun sanar da kotu cewa mun mika wa gwamnatin jihar takardun kotu tuntuni ba tare da mun ji daga gare su ba sai yanzu. Idan sun zabi mu sasanta a wajen kotu, to za mu sadu da su mu ga abubuwa da za su gabatar mana. Idan mun gamsu za mu dawo kotu mu nemi a yanke hukunci a a kan lamarin don kada ya zama maganar fatar baki. Idan muka yi haka mun san mun bi ka’idar da ta dace kuma ba za a cutar da al’ummarmu ba saboda wannan lamari ne da ya shafi ’yancin dan Adam”. Inji shi.