✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin iyaka tsakanin Abuja da Neja ya jefa mazauna Dakwa cikin matsala

Mazauna garin Dakwa da ke yankin da ke fama da rikicin iyaka a tsakanin Abuja da Jihar Neja, sun sake samun kansu a cikin matsala,…

Mazauna garin Dakwa da ke yankin da ke fama da rikicin iyaka a tsakanin Abuja da Jihar Neja, sun sake samun kansu a cikin matsala, bayan Ma’aikartar Kula da Birnin Tarayya Abuja ta rusa gidaje sama da 100 a yankin a makon jiya, sannan ta sa alama a wasu gidaje da suka kai 500 a ranar.

Matsalar ta shafi Unguwar Fulani ne, wani sabon yanki a garin da ke da gidajen alfarma kuma daura da babban titin da ya tashi daga garin Deidei zuwa Zuba.

Wakilinmu da ya ziyarci yankin a ranar Juma’ar da ta gabata, ya samu labarin cewa aikin rusa gidajen ya faru ne a lokacin da yawancin mazauna garin da yawanci ma’aikata ne da ’yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a cikin Birnin Abuja. Sai dai tun daga ranar da dama daga cikinsu sun kaurace wa wurarensu na aiki tare da gudanar da zanga-zanga da ta hana motocin aikin rusau samun damar shiga yankin ta hanyar killace hanya.

Wani jagoran mazauna wurin mai suna Bijida Malik da ya shaida wa waklinmu, cewa yawancinsu bayan sun sayi fuloti suna sama musu takardu daga Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja. Ya ce daukacin haraji da suke biya na tsawon shekara da tsarin zabubbuka da suke yi, na da alaka ne da Jihar Neja ba Abuja ba. Ya ce “Saboda haka abin mamaki ne Hukumar Birnin Tarayya ta yi ikirarin mallakan yankin a yanzu,” inji shi.

Sarkin Hausawan Dakwa, Injiniya Mukhtar Bello da shi ma ya halarci zanga-zangar a ranar, ya ce takaddama a kan ikon mallakar garin a tsakanin Abuja da Neja dadaddiya ce da ta kai shekara 20.

Ya ce sai dai kamar yadda ya faru a baya, za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun kare gidajensu ta hanyar hana motocin rusau shiga wurin.

A zantawarsa da Aminiya, Babban Daraktan Sashin Sa-ido Kan Gine-Gine na Birnin Abuja da ke gudanar da aikin na rusau, Malam Mukhtar Galadima ya zargi sarakunan gargajiya na yankin da sayar da filayen ba kan ka’ida ba. Ya ce filin da ake takaddama a kai na Unguwar Fulani a Dakwa girmansa ya kai kadada 204, kuma an tsara tare da bada shi a matsayin Kasuwar Sayar da Motoci ta Abuja  ce a shekarar 2011.

Ya ce an gudanar da aikin sharar fili tare da aikin rijiyar burtsatse a lokacin, sai dai a cewarsa bayan fuskantar matsalar korafi daga al’umma da ya ce takaddamar iyakan ya jawo, an jingine cigaban aikin a lokacin.

Malam Mukhtar Galadima ya ce tun daga lokacin wadansu suka ci gaba da yin gini da ya kai abin da ya rage yanzu bai wuce kashi 20 cikin 100 ba na filin ba. Sai dai ya ce a dalilin takaddamar, a yanzu za su sake jingine aikin har sai an warware lamarin da zai shafi kawo jami’an safiyo na fili daga Birnin Tarayya da kuma Jihar Neja.

Sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata, jami’an na Abuja sun yi yunkurin sake kutsawa yankin da motocin rusau, yayin da jama’ar garin kuma suka tare hanyar shiga wajen. Ana cikin haka ne sai Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ahmed Muhammed Ketso ya iso yankin don gane wa idonsa abin da ke faruwa lamarin da ya kwantar da hankali.

Mataimakin Gwamnan wanda ya samu rakiyar wadansu jami’an gwamnatin jihar, sun zagaya wuraren tare da tantance alamomin iyaka.

A jawabin da ya yi ya roki tarin jama’ar garin da ke cike da farin cikin ganinsa, su kwantar da hankalinsu tare da guje wa daukar doka a hannu. Ya ce Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello zai zauna da Ministan Abuja kan lamarin tare da samar da maslaha ta dindindin.