✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya ya jefa Kanawa cikin dar-dar

Tsattsamar dangantakar da ke ci gaba da gudana a tsakanin bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magajinsa Dokta Abdullahi Umar Ganduje…

Tsattsamar dangantakar da ke ci gaba da gudana a tsakanin bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magajinsa Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta kara muni a baya-bayan nan.

Dangantakar ta fara tsami ne bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dare mukamin kujerar mulkin jihar a ranar 29 ga Mayun shekarar 2011, inda har ta kai darewar Jam’iyyar APC gida biyu, wato APC Kwankwasiyya da APC Gandujiyya, lamarin da amsu fashin bakin siyasa ke hangen ba zai haifar wa jam’iyyar da mai ido ba a zabe mai zuwa badi.

Mutane daban-daban da kungiyoyin jama’a irin su Cibiyar Binciken Al’amuran Siyasa ta Jami’ar Bayero da ke Gidan Mambayya sun yi ta kokari wajen sasanta tsakanin bangarorin biyu, sai dai abin bai yi nasara ba, domin maimakon abin ya yi sauki sai ya dauki sabon salo inda bangarorin suke jifan juna da bakaken maganganu da yarfen siyasa musamman ta kafafen watsa labarai.

Yanzu lamarin ya sake daukar sabon salo inda aka fara fito-na-fito a duk lokacin da mabiya bangarorin biyu suka hadu a wuri guda, inda ba a wanyewa lafiya.


Abin da ya dada rura rikicin

A kwanakin baya an yi ta watsa wani faifan bidiyo a kafafen watsa sadarwar zamani inda ake zargin an ji muryar Kwamishinan Ayyuka na Musamman kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Alhaji Abdullahi Abbas yana yin wasu kalamai cewa a shirye suke za su dauki rigimar siyasa su bi Kwankwaso har cikin dakinsa da ita.

Wadannan kalamai da aka jingina ga Kwamishinan sun janyo hankulan masu fadi-a-ji a jihar da kuma kungiyoyin wanzar da zama lafiya kamar Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci gaban Al’umma (CITAD) inda suka yi ta kiraye-kiraye ga hukumomin tsaro su yi wani abu a kai. Sun ce idan har ba a yi wa tufkar hanci ba, to Allah ne kawai Ya san kare jini biri jinin da za a yi a tsakanin bangarorin biyu, ganin bayan kwana biyu da fitar wadancan kalamai an samu barkewar rikici a tsakanin magoya bayan bangarorin biyu inda mutane da dama suka samu raunuka. 

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da tayar da rikici ciki har da ’ya’yan Kwamishina Abdullahi Abbas tare da gayyatar Kwamshinan domin amsa wasu tambayoyi.

Sabanin da ya haifar da shugabannin bangarorin biyu na Jam’iyyar APC Gandujiyya a karkashin shugabancin Abdullahi Abbas da bangaren Kwankwsiyya a karkashin jagorancin Umar Haruna Doguwa, ya sa Majalisar Dattawa ta nada kwamiti a karkashin jagoancin Sanata Muhammad Magoro inda ya zo Jihar Kano don bincikar halin da ake ciki.

Kuma ana cikin wannan dambarwa ne Abdullahi Abbas ya yi murabus don radin kansa inda uwar jam’iyya ta kasa ta nada Injiniya Bashir karaye a matsayin sabon shugaban jam’iyyar. Sai dai har yanzu bangaren Kwankwasiyya na kan bakansa inda suke cewa wanda uwar jam’iyyyar ta turo dan bangaren Gandjiyya ne.

Rikicin ya sa bangaren Kwankwasiyya kafa jaridarsa Kwankwasiyya wada a ciki take watsa manufofinta, ganin cewa gwamnatin jihar ta farfado da jaridar Triumph da bangaren Gandujiyya ke amfani da ita a matsayin kafar watsa manufofinta da ta gwamnati.

A kwanakin baya bangaren Kwankwasiyya ya kaddamar da neman tallafi don kafa  Gidauniyar Kwankwasiyya inda aka tara Naira miliyan 41 domin yin amfani da kudin wajen tallafa wa daliban jihar da ke karatu a kasashen waje wadanda suke korafe-korafe cewa gwamnatin jihar ta gaza biya musu kudin karatu. Mafi yawan daliban dai gwamnatin da ta shude ce ta dauki nauyin karatunsu a kasashe daban-daban, lamarin da gwamanti mai ci ta dora a kai. Sai dai a kwanan baya daliban sun shiga kafafen watsa labarai suna neman gwamnati ta agaza musu don biya musu kudin makaranta da na abinci da sauransu inda suka nuna cewa gab suke su rasa damar karatun dungurumgum.

Wannan kiraye kiraye da daliban ke ta yi ya sa bangaren Kwankwasiyya ke zargin gwamnatin da gazawa wajen biya wa daliban kudin karatunsu saboda gwamnatin Kwankwasiyya ce ta kai daliabn kasashen wajen, zargin da gwamnati ta sha musantawa inda ta dora alhakin rashin biyan kudin karatun daliban a kan karyewar tattalin arziki da ya shafi jihar da kasa da duniya baki daya.


Ziyarar da Kwankwaso zai Kano

A ’yan kwanakin nan lamarin ya sake muni sakamakon gabatowar ranar da madugun Kwankwasiyya zai kai ziyara jihar wadda aka shirya yi a ranar 30 ga Janairun na, kuma aka ce magoya bayansa za su tarbe shi a garin Chiromawa da ke karamar Hukumar Garun Malam.

Bayan sanya waccan ranar taro da bangaren Kwankwasiyya ya yi ne sai aka wayi gari da sanarwa daga bangaren gwamnati da Jam’iyyar APC cewa za su gudanar da taron siyasa a daidai wancan rana, lamarin da ’yan Kwankwasiyya ke gani a matsayin takalar fada.

Hajiya Binta Spikin daya daga ckin masu taimaka wa Sanata Kwankwaso a harkar watsa labarai ta tabbatar da batun zuwan Kankwason a ranar 30 ga Janairu “Duk da cewa mun ji bangaren Gandujiyya na yada jita-jita cewa maigidanmu ba zai zo Kano ba. Ina tabbatar muku cewa maigidanmu zai zo Kano a ranar 30 ga Janairu ba fashi. Zai zo domin ya taimaka wa ’ya’yan jam’iyyarmu game da zaben kaanan hukumomi mai zuwa.”

Sai dai Sakataren Jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Ibrahin Zakari Sarina ya ce Jam’iyyar APC ta sanya ranar 30 ga wata ne don raba tuta ga ’yan takara a garin Kwanar dangora wadda ta zo daidai da jadawalin yakin neman zabe da Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KAINSEC) ta fitar a shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi da za a yi nan ba da dadewa ba. “Da a ce Kwankwaso ya sanar da jam’iyya game da taron da zai yi wanda ya yi daidai da ranar da za mu gudanar da namu taron da jam’iyya ta dage nata taron zuwa wata rana ta daban. Amma saboda bai sanar da jam’iyya ba muka sanya namu tarurrukan daidai da jadawalin KAINSEC,” inji shi.


Tarurrukan biyu barazana ne ga zaman lafiya

Aminiya ta tattauna da mashawarcin Gwamna Abdullahi Ganduje kan Al’amuran Ruwan Sha, Honorabul Anas Abba Dala game da hangensa kan haduwar tarurrukan bangarorin biyu inda ya ce abu ne mawuyaci bangarorn siyasa masu adawa da juna su hadu a wuri daya kuma a lokaci guda ba tare da wani abu na rashin dadi ya auku ba. “Zai yi wuya a ce masu adawa su hadu a wuri guda ka yi tunanin a gama lafiya. A duk inda ake dimokuradiyya a duniya idan za a hadu da abokan adawa a wuri daya, idan ba Allah ne Ya kiyaye ba, to fa sai abin da ka gani,” inji shi.

Ya yi kira ga bangarorin biyu a matsayinsu na jagororin al’umma su duba al’ummarsu, daya ya janye wa daya batun taron don a samu wanzuwar zaman lafiya. “Ni a ra’ayina ina ganin a matsayinsu (Ganduje da Kwankwaso) na shugabannin al’umma su duba masalahar al’ummarsu, dukansu ’yan Kano ne. Duk abin da mutum zai yi ya san cewa zai iya zama sanadiyar wani ya rasa rai ko lafiya ko dukiya, to kamata ya yi ya hakura da shi. Zai fi kyau a cikinsu wani ya janye wa dan uwansa domin masalahar al’umma wannan shi ne zai sa a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar,” inji shi

Taron bangarorin biyu a rana daya a kuma wurare da ba su da nisa ya jefa tsoro a zukatan al’ummar jihar saboda rashin sanin abin da taron zai haifar.

Rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya ya dada jefa al’ummar Jihar Kano cikin dar-dar ne sakamakon karatowar zaben kananan hukumomin jihar, inda bangarorin biyu suka sayar wa ’yan takararsu fom-fom din tsayawa takarar a Jam’iyyar APC, inda ake ganin hakan na iya haifar da rikici a lokacin zaben.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a wajen tarurrukan biyu wanda kowane bangare ya tsaya kai da fata zai gudanar a ranar 30 ga watan Janairun ba tare janye wa juna ba.