✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldhinho ya tsiyace

Rahotanni da ke fitowa daga Brazil sun nuna tsohon dan kwallon Brazil Ronaldhinho ya shiga mawuyacin hali, bayan wata kotu da ke Brazil ta ci…

Rahotanni da ke fitowa daga Brazil sun nuna tsohon dan kwallon Brazil Ronaldhinho ya shiga mawuyacin hali, bayan wata kotu da ke Brazil ta ci tararsa tare da dan uwansa Roberto Fam Miliyan 1 da dubu 700 kwatankwacin Naira Miliyan 613 da dubu 700 saboda laifin gina wani kamfanin sukari a filin da ba su samu amincewar gwamnati ko wata hukuma ba. Tun a 2015 kotun ta zartarwa dan kwallon da dan uwansa wannan hukunci, amma har yanzu ya kasa biyan tarar.

Kamar yadda jaridar Mail online ta yanar gizo ta kalato a ranar Litinin da ta wuce, ta ce kotun ta sake fusata bayan ta lura dan kwallon ya ki biyan wannan tara, inda ta shiga yin binciken kwakwaf a asusun ajiyarsa na banki.  Sai dai abin mamaki da tashin hankali shi ne yadda kotun ta gano dan kwallon ya tsiyace, kuma asusun ajiyarsa yana dauke ne da kudin da ba su wuce Fam 5 ba kwatankwacin Naira dubu 1 da 805.

Bincike ya nuna dan kwallon ya shiga matsala ne bayan ya rika biyan basussukan da ake bin sa a boye ba tare da sanin kowa ba.

Kamar yadda mai gabatar da kara a kotu ya shaidawa manema labarai ya ce “Bayan an gudanar da bincike ne aka gano dan kwallon bai da isasshen kudin da zai iya biya tarar da aka yi masa ta Fam Miliyan 1 da dubu 700 kwatankwacin Naira Miliyan 613 da dubu 700, inda aka tarar da Fam 5 kwatankwacin Naira dubu 1 da 805.  Hakan ya sa kotun ba ta da wani zabi da ya wuce ta kwace fasfot (Password) din sa tare da na dan uwansa har sai sun biya tarar.”

Kotun ta ce za ta kwace fasfot din Ronaldhinho da zarar ya koma Brazil daga tafiye-tafiyen da yake yi a halin yanzu. Ronaldhinho dai ya taba buga wa manyan kulob a Nahiyar Turai da suka hada da Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa da FC Barcelona da ke Sifen da kuma AC Milan na Italiya.

A 2005 ne ya taba zama Gwarzon dan kwallon duniya a lokacin da yake buga wa kulob din FC Barcelona na Sifen kwallo.  Ya buga wa Brazil wasanni har sau 97 inda ya zura kwallaye 33 a raga.

A 2011 ne ya yi ritaya daga yin kwallon kafa, inda ya koma Brazil da zama, al’amarin da ta sa tun daga wancan lokaci ne al’amarran rayuwa suka fara yi masa zafi. A baya an ruwaito yana da sha’awar tsayawa takarar Sanata.  Sannan kanwarsa ta taba yin korafin yadda ya ajiye wadansu ’yan mata biyu a katafaren gidansa kuma ya rika ba su makudan kudi duk wata da niyyar aurensu a rana daya kuma a lokaci daya, abin da ta ce ya saba da al’adar gidansu.

Wannan da ma wadansu dalilai na yin facaka da kudi ne suka jefa tsohon dan kwallon cikin mawuyacin hali.