✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo na sha’awar komawa Madrid

Fitaccen dan kwallon  nan na duniya dan kasar Portugal kuma tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid da Manchester United, Cristiano Ronaldo ya bayyana sha’awarsa…

Fitaccen dan kwallon  nan na duniya dan kasar Portugal kuma tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid da Manchester United, Cristiano Ronaldo ya bayyana sha’awarsa ta sake komawa kulob din Real Madrid da ke Spain.

A wata hira da abokinsa kuma  dan jarida, Edu Aguirre ya yi da gidan talabijin na Chiringuito na Spain a ranar Lahadin da ta wuce ya ce hakika abokinsa Ronaldo ya shaida masa yana sha’awar komawa Madrid nan gaba sai dai bai bayyana takamaiman lokacin ba.

Ronaldo wanda ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallo a kulob din Madrid bayan ya zura kwallo 451 a raga kafin ya koma kulob din Jubentus da ke Italiya  yana daga cikin wadanda suka kalli wasan El-Clasico a tsakanin kulob din Real Madrid da FC Barcelona a ranar Lahadin da ta wuce.

Sai dai Edu ya tabbatar da cewa yanzu hankalin Ronaldo ya fi karkata ne wajen taimaka wa kulob din Jubentus a kakar wasa ta bana amma komai zai iya faruwa game da sake komawarsa Madrid nan gaba.