Da Dumi Dumi

Ronaldo ya sayi agogon Naira miliyan 174

Fitaccen dan kwallon nan dan  Fotugal da yanzu ke buga wa kulob din Jubentus na Italiya kwallo, Cristiano Ronaldo ya sayi wani agogo kirar Roled da aka kiyasta kudinsa a kan Fam dubu 371 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 174.

Dan kwallon ne ya sanar da wannan labari a shafin sada zumuntarsa na Instagram a ranar Litinin da ta wuce.

Rahotanni sun ce Kamfanin Roled da ya kera agogon, bai taba kera agogon da ya kai wanda Ronaldo ya saya tsada a tarihi ba.

Ronaldo mai shekara 34, dan kwalisa ne da ke amfani da kayayyaki masu tsada da suka hada da motoci da tabarau da agogo da ’yan kunne da tufafi da kuma takalma.  Yana daga cikin wadanda manyan kamfanoni ke amfani da su wajen yi musu tallace-tallace saboda matsayinsu.

ADVERTISEMENT
Share