✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunonin ’yan sanda da kwastam sun kama harsashi dubu 60 a Jihar Oyo

Rundunonin tsaro na ’yan sanda da kwastam a Jihar Oyo, sun kama harsasan bindiga masu rai, fiye da dubu 60 a wani samame daban-daban da…

Rundunonin tsaro na ’yan sanda da kwastam a Jihar Oyo, sun kama harsasan bindiga masu rai, fiye da dubu 60 a wani samame daban-daban da suka yi a yankin garin Saki da ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Benin.
’Yan sanda, sun ce sun kama harsashi 3,525 ne, a yayin da rundunar kwastam ta kama harsashi 56,750 duk a wannan wata na Mayu.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a ofishinsa, Kwamishinan ’yan Sanda na Jihar Oyo, Muhammed Abdulkadir Indabawa ya ce, “Babban jami’in ’yan sanda (DPO) na yankin Saki, ya jagoranci  jami’ansa na sintiri a unguwar Isale Adini, suka yi arba da wata karamar mota mai lambar AW 965 KTU, wacce duk mutum biyar da ke cikinta suka fice a guje, amma an kama daya daga cikinsu mai suna Soliu Akanji. Daga bisani aka gano harsasai guda 3,525 a cikin motar. Za a durkusar kamammen a gaban kotu bayan kammala bincike”.
A yayin da yake nuna kamammun harsasan ga ’yan jarida a ofishinsa, Kwamandan rundunar kwastam a jihohin Osun da Oyo, Kwanturola Richard Oteri, cewa ya yi jami’ansa sun samu nasarar kama katon-katon 227 da ke dauke da harsasai masu rai, 56,750 ne a kan hanyar Igboho a garin Saki. Ya ce duk da yake babu wanda aka kama dangane da wannan al’amari, sai dai, “Mun gano irin dabarar da aka yi wajen lullube harsasan a karkashin tulin busassun rogo da aka yi badda-kama domin tsallake shingen bincike da muke yi.” Inji shi.
Mataimakin kwamishinan ’yan sanda Musa Kimo, shi ne ya karbi harsasan daga hannun Kwanturola Oteri, wanda ya jinjina wa jami’ansa a kan nasarar da suka yi, musamman a daidai lokacin da harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya.
A wani labari daban, kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammed Indabawa ya ce rundunar ’yan sanda a jihar ta kama mutane 4 da suka kware wajen kwace manyan motoci masu dakon buhunan siminti suna karkatar da akalarsu zuwa garin Oyo domin sayar da satattun simintin ga dillalan zaune. Da yake nuna barayin, wadanda aka lullube fuskarsu, kwamishinan ya ce, asirinsu ya tonu ne a ranar 15 ga wannan wata, lokacin da rundunar yaki da fashi da makami (SARS) ta samu labarin karkatar da akalar wani direban tirela da ke dauke da buhunan siminti guda 600 da aka nuna masa bindiga kafin a kwace kayan. Rundunar ta fara bin diddigi da yin binciken kwakwaf har ya kai ga kama mutane biyu, Seun Ogundele da Femi Johson, wadanda suka bayyana sunayen dillalan siminti da ke zaune a garin Oyo, Tajudeen Hammed da Bode Ogunmola, wadanda aka kama, aka karbo buhunan siminti guda 1,200 da suka saya daga hannun barayin. Su da kansu barayin ne suka yi bayanin wuraren da suka jefar da manyan motocin, bayan sun kwashe satattun buhunan na siminti, inji kwamishinan, wanda ya ce za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.