✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rwanda ta kafa kyakkyawan misali

A wani yunkuri da ta yi na kara hadin kai da kara dankon zumunci a tsakanin kasashen Afirka, Gwamnatin Rwanda a cikin wata biyu da…

A wani yunkuri da ta yi na kara hadin kai da kara dankon zumunci a tsakanin kasashen Afirka, Gwamnatin Rwanda a cikin wata biyu da suka gabata ta karbi ’yan gudun hijirar kasashen Afirka 189 da suka makale a kasar Libiya a yunkurinsu na zuwa kasashen Turai. ’Yan gudun hijirar da suka hada da yara 59 suna daga cikin kashin farko na ’yan gudun hijira 500 da kasar ta yi alkawarin za ta ba su mafaka a karkashin wata yarjejeniyar fahimtar juna da kasar ta sanya hannu da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da kuma hadi gwiwar Babban Kwamishina Mai kula da ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

A karkashin wannan yarjejeniya dai, gwamnatin Rwanda ta amince za ta ba ’yan gudun hijirar mafaka a yayin da a gefe daya kuma za a ci gaba da bin matakin sama musu mafita a kasashen da suka ci gaba. Wannan ya kunshi samar musu da matsuguni tare da ba su damar komawa zuwa kasashensu na asali ga wadanda suke son yin haka da kuma ba su damar yin cudanya da jama’ar Rwanda ba tare da tsangwama ba. Kungiyar Tarayyar Afirika ce za ta dauki dawainiyar aiwatar da haka a yayin da Hukumar  Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) za ta dauki nauyin biyan kudin jirgi da samar da sauran kayayyakin da ake bukata a yayin zamansu a sansanin da za a samar musu.

Wannan shiri dai Rwanda ta kirkiro da shi ne domin ta karbi ’yan gudun hijira na Afirka wadanda suka makale a kasar Libya a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai. Shugaba Paul Kagame ya ce kasar Rwanda ta yanke shawarar yin haka ne a matsayin wani mataki na nuna kyakkyawan misali. Ya ci gaba da cewa bada mafaka ga ’yan gudun hirar kasashen Afirka da suka makale a wasu gidajen kaso na kasar Libya wani kyakkyawan misali ne da yake nuna yadda kasashen Afirka za su iya magance matsalolinsu a tsakaninsu. Kuma ya yi kira ga sauran kasashen Afirka su dauki irin wannan mataki. Ma fi yawan ’yan gudun hijirar da suka isa Rwanda sun fito ne daga kasashen Sudan da Somaliya da Habasha.

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yaba wa wannan mataki na kasar Rwanda sannan ta kira shi da cewa wani yunkuri ne da wata kasa ta Afirka ta yi domin ta kawar da wata matsala da Nahiyar Afirka take fama da ita. Kwamishinan Harkokin Zamantakewa ta AU, Amira Elfadil ta ce “Wannan wani sabon babi ne a bangaren tarihi, inda ’yan Afirka suke taimaka wa ’yan uwansu ’yan Afirka. Kullum muna ta maganar yadda za mu samar da sahihiyar hanya ta magance matsalolinmu, kuma ina sa ran wannan ya kasance daya daga cikin wadannan hanyoyi.” Ta kuma yi fata za a sake samun karin wasu kasashen Afirka da za su yi irin wannan hobbasa don taimaka wa masu gudun hijira da masu neman mafakar siyasa daga Afirka.

Kamar yadda Hukumar UNHCR ta fitar akwai kimanin ’yan gudun hijira 5,000 da suka makale a gidajen kaso na kasar Libiya. Ma fi yawansu kuma ana zargin ana cin zarafinsu ta hanyar fyade da yi musu azaba tare da sanya su aiki mai tsanani. Akwai kuma ’yan Afirka da dama wadanda suka makale a wasu kasashen a yunkurinsu na h aurawa zuwa Nahiyar Turai. Da yawa daga cikinsu an sayar da su a matsayin bayi yayin da da dama kuma sun rasa rayukansu a yayin da suka fada cikin hadari na jiragen da ke dauke da su cikin Tekun Maliya zuwa kasashen Turai.

Kadan daga cikinsu da suka samu sa’ar kaiwa ga gaji suka tsinci kawunansu  a gabar Tekun Italiya suna fuskantar kin amincewa da su a matsayin masu neman mafakar siyasa da kasashen Turai ke yi. Daga karshe kuma su tsinci kansu a sansanin gudun hijira na dole. Don haka wannan wani ci gaba ne ga Kungiyar AU da Hukumar UNHCR ganin yadda kasar Rwanda ta dauki nauyin wadansu daga cikin ’yan gudun hijirar. Wannan yunkuri na Rwanda ya zo da ba-zata ganin yadda kasar ke kokarin farfadowa daga kisan kare-dangin da ya auku a kasar wanda ya ci rayukan ’yan kasar kimanin miliyan daya shekara 25  da suka gabata.  Haka Rwanda a halin yanzu tana bayar da mafaka ga wadanda suka guje wa rikice-rikicen siyasa da suke faruwa a kasashen Jamhuriyyar Kwango da Burundi. Wannan yana nuna cewa har yanzu a akwai sauran shugabannin Afirka wadanda suke da muradin kawo hadin kai da taimakon juna a cikin kasashen. Sannan wannan wani sako ne da ke nuni da cewa ba sai kasa tana da arziki sosai ba sannan za ta iya taimaka wa wata kasa.

A wannan yanayin da ake ciki wanda maganar rikicin nuna kyamar bakar fata da bakaken fata ke yi wa junansu aAfirka, saurann kasashen Afirka ya dace su gaggauta yin koyi da kasar Rwanda wajen taimakon juna. Muna fatar wannan kyakkyawan misali da Shugaban Rwanda Paul Kagame ya nuna zai zama abin koyi ga sauran shugabannin kasashen Afirka.