✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sababbin shugabannin kananan hukumomin Jihar Nasarawa 10 sun saba laya

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za ta ci gaba da yin biyayya ga dokokin kasar nan musamman wadanda suka shafi kananan hukumomi. Gwamnan Jihar Umaru…

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za ta ci gaba da yin biyayya ga dokokin kasar nan musamman wadanda suka shafi kananan hukumomi. Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ne ya fadi haka a gidan gwamnati da ke Lafiya lokacin bikin rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi 10 da aka zaba a ranar Asabar da ta gabata.
Gwamnan wanda ya bayyana zaben a matsayin mai cike da babban tarihi kasancewa an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali, ya jinjina wa Hukumar Zabe ta Jihar kan wannan babbar nasara da ta samu. Ya ce kasancewar kananan hukumomi sun fi kusa da al’ummar karkara ya zame wa gwamnatinsa wajibi ta ba su fiffiko don a rika damawa da mazauna karkara.
Ya shawarci sababbin shugabannin kananan hukumomin su tabbatar sun sauke nauyin da ke wuyansu na samar wa al’ummarsu ababen more rayuwa don samun ci gaba mai dorewa, kuma su kirkiro da hanyoyin tara kudaden shiga don taimaka wa kansu maimakon su dogara ga gwamnatin jihar. Ya ce jihar tana daya daga cikin jihohin da suke da karancin kudin kaso daga tarayya.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da zama lafiya don ba gwamnatinsa damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya.
Da yake jawabi a madadin sababbin shugabannin, shugaban karamar Hukumar Doma, Mista Henry Omaku, ya jinjina wa hukumar zabe ta jihar dangane da gudanar da zaben da ya bayyana a matsayin mai cike da gaskiya, inda ya ba da tabbacin za su yi kokarinsu don samar wa al’ummominsu ribar dimokuradiyya don inganta walwalarsu.
Ba a kammala zabe a kananan hukumomi 3 da suka rage ba wato Akwanga da Obi da Nasarawa ba.