Da Dumi Dumi

Sai yanzu jami’an tsaro suka san da gidajen mari?

Ranar Alhamis 26 ga Satumban da ya gabata ne Rundunar ’Yan sandar Jihar Kaduna ta yi dirar mikiya ga wata cibiyar horarwa da tsugunar da kangararrun yara mai suna Imam Ahmad bin Hambal da ke Titin Mai Dubun Tsumma a garin Rigasa da ke  Karamar Hukumar Igabi, inda ta yi awon gaba da dalibai ko mazauna cibiyar 190, wadanda 77 daga cikinsu kananan yara ne  da kuma malaman cibiyar guda bakwai.

’Yan sandan sun ce sun tarar da wadanda ake tsare su a cibiyar cikin mawuyacin hali na yunwa da azabtarwa da bautarwa, baya ga kasancewarsu cikin kazantar jiki da  muhalli da ke fama da cinkoso. Wadansu daga cikin tsararrun inji ’yan sandan a Mari suke jiddin wala hairan.

Jin wannan kamu ke da wuya, sai aka ji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana ba da sanarwar yin jinjina ga Rundunar ’Yan sandan ta Kaduna a kan namijin kokarin da ta yi wajen gano waccan cibiya da  kamun da ta yi. Abin da Shugaba Buhari ya yi tir da Allah wadai kan yadda ake tafiyar da cibiyar, sannan ya ba da umarni ga Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta ci gaba da baza komarta a duk fadin kasar nan don gano irin wadannan cibiyoyin azabtarwa da bautar da yara. Yana kurarin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata ayyukan ta’addaci da cin zarafin dan Adam ba.

Mai yiwuwa samun wannan jinjina da yabo da kuma umarni na Shugaban Buhari ya sanya  yanzu rundunonin ’yan sandan jihohi da jami’an tsaro na farin kaya (NCDSC), suka tashi tsaye wajen  kai hare-hare a cibiyoyin mari, musamman a jihohin Arewa.

Misali a Jihar Kaduna ’yan sandan sun sake kai hari a wata cibiyar mari da ke garin Rigasa inda suka kwashe mutanen da ke cibiyar suka kama malamanta. A Zariya ma jami’an tsaro sibil difens sun kai hari wata cibiyar mari a Unguwar Limanci, cibiyar da masu kula da ita suka ce gadon tafiyar da ita suka yi daga mahaifinsu marigayi Malam Aliyu da Allah Ya yi wa rasuwa shekara hudu.

ADVERTISEMENT

A Jihar Katsina rundunar  ta kai samame a Cibiyar Mari ta Malam Niga da ke cikin Unguwar Kofar Durbi a birnin Katsina, sannan ta leka birnin Daura, inda ta auka wa Cibiyar Mari ta Malam Bello da aka fi sani da Bello Mai Kawarin Daura. A dukkan wadannan cibiyoyi, ’yan sandan sun kubutar da dalibansu da kuma kama malaman da yanzu aka gurfanar gaban shari’a kan tuhumar tsarewa da cin zarafin mutane da  suka ce hakan ya saba wa sashe na 257 (b) da na 270, na Kundin Manyan Laifuffuka na Final Kod.

A waccan cibiya ta Daura ’yan sandan sun yi zargin ana luwadi da wadansu kananan yara da ke cibiyar, zargin da Malam Bello ya musanta.

Hakazalika, rahotanni sun tabbatar  zuwa yanzu rundunonin ’yan sandan jihohin Adamawa da Kwara, sun kai irin wannan samame a wasu cibiyoyin ’yan mari a Yola da Ilorin. A can din ma sun yi nasarar tarwatsa cibiyoyin biyu, tare da kubutar da dalibai da kame malaman cibiyoyin.

A daidai wannan gaba ’yan kasa mun kasa kunne muna jiran jin wace jiha da wace kuma za mu ji ’yan sanda za su dira, kuma su wa da wa suka tarar da kuma wane irin hukunci aka yanke wa masu irin wadancan cibiyoyi da ko hukuncin zai iya kawo karshen kafa cibiyoyin mari a kasar nan, ko a’a, ko ma yakin da gwamnatin ta daura da masu cibiyoyin marin zai dore, ko shiriricewa zai yi?

Kafin Allah Ya kai mu ji da ganin amsoshin wadannan tambayoyi ya kamata mu  dubi tarihi da matsalolin kafa cibiyoyin mari a Arewacin kasar nan.

A cikin shirin BARKA DA HANTSI na gidan Rediyon Freedom da ke Kano an ji Khalifa Mutawakkil Baba Saleh Limamin Sharifai kuma Sakataren Kudi na Kungiyar Makarantun Tarbiyya da ke Kano (makarantun da kafin ’yan sanda su fara kai wa cibiyoyin mari hari aka sansu da cibiyoyin mari a Kano), ya ce su a Kano yau sama da shekara 200 a gidansu da wasu unguwanni ake tafiyar da cibiyoyin mari, yana mai cewa Shehu Usman Dan Fodiyo (Allah Rahamshe shi) ya taba kawo wa cibiyarsu ziyara. Ya kara da cewa ai ba wani abu ya sa aka kirkiri cibiyoyin mari ba, sai don yadda za a rika gyara tarbiyyar yara da mutanen da suka zama kangararru, kamar barayi da ’yan fashi masu tare hanya da shan miyagun kwayoyi da ayyukan gagara.

Khalifa Mutawakkil ya ce a wannan aiki na gyaran tarbiyya masu cibiyoyin mari suke kai, musamman yanzu da tarbiyya da ayyukan badala da na shaidanci suke kokarin game kasa baki daya musamman tsakanin matasan kasar nan da kuma nuna halin  ko-in-kula na iyaye wajen daukar dawainiyar ’ya’yansu. Shi ma Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Yaki da Fatauci da Bautar da Jama’a ta Kasa (NAPTP), a Jihar Kano, Alhaji Aliyu Abba Kalli, a tasa gudunmawar cewa ya yi gwamnati ba hana gudanar da cibiyoyin mari take son yi ba, illa dai tana son ta gyara tsarin ne.  Ya nemi masu cibiyoyin mari ko masu son kafa sababbi  su rika tuntubar hukuma don samun izini  da sauran shawarwari, yana mai cewa dukkan cibiyoyin marin da suka yi wa dirar mikiya a jihohin Kaduna da Katsina zuwa yanzu, ba a gudanar da su bisa sharuddan da su kamata ba, kuma cike suke da ayyukan cin zarafin dan Adam.

Koma dai yaya cibiyoyin marin suke ciki, in an bi ta barawo sai a bi ta mabi sawu. Lalura ta sa iyaye shekaru aru-aru a kasar Hausa suke daukar kangararrun ’ya’yansu su kai cibiyoyin mari, musamman bisa ga imanin da iyayen suka yi na cewa a cibiyoyin ana aiki da Alkur’ani Mai girma ne mai cike da dimbin shiri, sannan uwa uba iyayen na ganin samun shiriyar ’ya’yan nasu, duk kuwa da azabtarwar da mahukunta ke zargin ana yi wa yaran.

Saura da me? Babban aikin da ke gaban iyaye bai wuce kara tashi tsaye wajen ganin ingantuwar tarbiyyar ’ya’yansu ba. Mahaifin da kaddara ta fada wa dansa ya kangare, to ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya ceto shi. Ga mahukunta kamata ya yi su kara yunkuri wajen samar da cibiyoyin gyara tarbiyya da koyar da sana’o’in hannu musamman ga matasa, kasancewar yanzu maganar da ake yi Gwamnatin Tarayya da na jihohi ba su da ingantattun irin wadannan cibiyoyi. Rashin cibiyoyin ne ke sa iyaye kai kangararrun ’ya’yansu cibiyoyin mari.

Ko kadan bai kamata jami’an tsaron kasar nan su ce duk tsawon lokacin da aka kwashe ana gudanar da cibiyoyin mari sai yanzu suka gano a kan haramtacciyar hanya ake gudanar da su.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya