Search
Subscribe
Sakwara da miyar karfasa

Sakwara da miyar karfasa

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara da maigida? Tare da fatan ana hakuri. Allah Ya sa mu dace amin. A yau na kawo muku yadda ake  sakwara da miyar kifi. Za a iya yi wa maigida wannan girki da rana ko dare ko don tarbar  manyan baki.

 

Abubuwan da za a bukata

•  Doya

•   Kifi; karfasa

•   Manja

•   Barkwano

•   Albasa

•   Magi

•   Kori

•  Garin tafarnuwa

 

HaDi

Uwargida ta fere doya sannan ta wanke ta Dora a wuta har sai ta yi laushi.  Sannan sai ta Dauko turminta tana jefa dafaffiyar doyar tana dakawa har sai ta yi laushi. Za ta iya zuba ruwan zafi domin samun sakwara mai laushi.

A yanka albasa sannan a daka barkono ya yi laushi sosai kuma a wanke kifi yadda ba za a ji karninsa ba. A Dora tukunya a wuta sai a zuba manja. Sannan a zuba albasa ta Dan soyu sannan a zuba jajjagen tumatir har sai ya soyu. Sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da kuma dakakken barkono

A zuba kifin sannan ruwa kaDan. Sai a rufe bayan mintin talatin sai a sauke.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin