✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sama da mutum 100 ke neman mukaman Kwamishinoni a Kano

Sama da mutum 100 ne ke yunkurin samun mukaman Kwamishinoni, wadanda suka hada da: ‘Yan siyasa, ma’aikata a harkar ilimi da kwararru a fannoni da…

Sama da mutum 100 ne ke yunkurin samun mukaman Kwamishinoni, wadanda suka hada da: ‘Yan siyasa, ma’aikata a harkar ilimi da kwararru a fannoni da dama ke neman mukaman Kwamishinoni a gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, ‘yan siyasar masu neman mukaman sun fito ne daga uban gidajen su da suka hada da: Tsohon Gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau  da tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar da tsohon Kwaminshinan Filaye Akitek Aminu Dabo.

Wata majiya ta sanar da rahoton cewa, a kalla kashi 40 cikin 100 ne ke saran dawo wa mukamansu na baya.