Da Dumi Dumi

Sama da mutum 140 ake tsoron sun rasu a hadarin jirgin ruwan Kamaru da na Libya

Wani karamin jirgin ruwan da ya yi hadari a tekun Bahar Rum
Wani karamin jirgin ruwan da ya yi hadari a tekun Bahar Rum

Fiye da mutum 100 ne ake fargabar sun rasu rayukansu, bayan hadarin wani jirgin ruwan Kamaru a cikin teku a ranar Lahadin da ta gabata.

Wasu majiyoyin Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) a Marina Legas sun ce jirgin ya bar Kalaba a Jihar Kuros Riba ta Najeriya ne zuwa Kamaru dauke da fasijoji 180 a ranar Lahadi amma bai isa inda ya nufa ba.

A ranar Litinin da manema labarai suka je inda jirgin ya tashi sun iske wadansu mutane suna tattauna batun hadari cikin jimami.

Kuma har zuwa tsakar rana ba a bar manema labari su shiga cikin tashar da jirgin ya tashi ba.  Bayanai sun ce jirgin ya tashi ne daga tasha ta C ta NPA da ke Kalaba ta hannun kamfanin Shoreline Logistics da misalin karfe 4;15 na yammacin Lahadi kafin hadarin ya auku.

Wata majiya ta ce sun samu labarin cewa hadarin ya auku ne a yankin ruwan Kamaru, amma duk da haka suna bincikar

ADVERTISEMENT

Wannan lamari yana zuwa a daidai lokaci da wani jirgin ruwa  ya yi hadarin da akalla mutum 40 suka rasu a gabar ruwan Libya, kamar yadda bayanan Hukumar ’Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), suka nuna.

“Mun samu wani mummunan labari da ke nuna asarar rayuka sakamakon hadarin jirgin ruwa a gabar tekun Libya,” inji Charlie Yadley, Kakakin Hukumar  UNHCR.

“Kimanin mutum 60 aka ceto; kuma an mayar da su kan tudu. An kiyasta kimanin mutum 40 ko dai sun mutu ko sun bace bat,” inji shi.

Bayanan na zuwa ne bayan, kakakin rundunar tsaron kan iyakar ruwan Libyan, Ayoub Gassim, ya fada wa Kamfanin Dillacin Labarai n AP cewa, an gano gawawwakin mutum biyar ciki har da wani yaro a kusa da garin Khoms da ke da tazarar kilomita 120 gabas da Tripoli, babban birnin kasar.

Ya ce an ceto kimanin mutum 65 galibinsu ’yan Sudan kuma ana ci gaba da nemo wadanda suka bace. Wadanda suka tsira daga  hadarin, sun hadar da mutanen kasashen Masar da Moroko da Tunisiya, kamar yadda Yadley ya nuna.

Wata kungiyar agaji mai taimaka wa masu ketare tekun Bahar Rum, mai suna Alarm Phone, ta ce mutum 100 ne ke kan jirgin ruwan da ya kifen, wadanda akasari suna kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai ne.

Share