Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sana’a tana da muhimmanci ga ‘ya mace – Amina Waziri

Amina Umar Waziri wata matashiya ce da ta yi fice kan sana’o’in hannu da kuma kungiyoyi daban-daban da suka shafi na tallafa wa marayu da gajiyayyu da wayar da kan jama’a da sauransu. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana mahimmancin sana’a ga mata da kuma irin nasarorin da ta samu a harkokin sana’o’i da kungiyoyin da take ciki. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka: 

ADVERTISEMENT

 

Takaitacciyar tarihin rayuwata:

ADVERTISEMENT

Ni dai sunana Amina Umar Waziri, amma an fi sani da Amina Waziri Kaduna. An haife ni a shekara ta 1990 a garin Kaduna. Amma mahaifina dan asalin Jihar Kano ne, sannan ita kuma mafiyata ‘yar asalin Jihar Benuwai ce. Sannan na taso cikin kula da tarbiyya karkashin su, kasancewar su masu son baiwa ‘ya’yansu tarbiyya har ma yaran makwafta, kuma wannan halayya ta mahaifana sun haska min rayuwa matuka bayan da na girma. Sannan na yi karatun Nazari da Furamare a makarantar Kwalejin Abubakar Gumi da ke Kaduna. Daga nan na zarce makarantar Sakandare ta Tafawa Balewa, da ke Kabala Costain a nan garin Kaduna, na yi karatu na karamar sakandare da babbar sakandare. Haka kuma na yi karatun Islamiyya, inda na samu damar sauke Alkura’ani mai girma, da kuma sauran daruwan da suka hada da Hadisi, Fikhu da Sira da sauransu.

 

Daga nan sai na tsinci kai na, a harkar koyon sana’o’in hannu daban-daban, kamar dinki da man shafawa da Sabula da dafa abinci musamman na bukukuwa da sauran taruka da dai sauransu. Daga nan sai na yanke shawarar komawa makaranta don zurfafa ilmi, abode an nuna min cewa muddin mace ta yi ilmi, to kamar ilmin al’umma ce baki daya, inda na shiga makarantar koyon kwanfuta, bayan da na kammala na yi aikin sanin makamar aiki a majalisar dokoki ta jihar Kaduna zuwa wani lokaci. Daga nan sai na shiga Jami’ar Ahmadu Bello, inda na yi karatun Difloma a fannin nazarin harkokin mulki. Sannan kuma a yanzu haka ina nan ina ci gaba da karatun digiri a wannan jami’a a kuma wannan fannin. Sannan kuma ina ci gaba da gudanar da harkokin sana’o’i da kungiyoyi.

 

kungiyoyi:

Ina cikin kungiyoyi da dama da suka hada da “Majalisar Burin Zuciya” da “Ranar Mawakan Hausa Foundation” da “Hausa Fulani Youth Debelopment and Orientation Forum” da “Women For Peace in Nigeria” da “Nasarawa Inuwar Gamji all Season Farmers Multi-Purpose Cooperatibe Society” da “Rayuwarmu A Yau Awareness Cooperatibe Society” da “Musulunci ke Magana” da dai sauransu.

 

Abin da ya karfafa mani gwiwar rungumar sana’o’i da kungiyoyi:

Babban abin da ya karfafa mani rungumar kama sana’o’i, shi ne ni saboda kasancewa ta mace ce mai neman na kanta, don haka ba na jiran sai an yi mani wani abu, da na ke da bukata. A kowanne lokaci ina kokarin ganin na mallaki abin da na ke bukata, ba sai na jira wani ko wata ya yi mani ba. Sannan kuma a gaskiya ina da sha’awar sana’a tun kafin wannan lokaci. Don haka ban cika sha’awar aikin gwamnati ba. Don haka zuciyata ta rinjaye ni da kama sana’o’in hannu wadanda ko a cikin gida mace za ta iya yinsu, ba sai ta je ta cakudu da maza ba. Babu shakka sana’a ta na daga darajar mace. Domin yanzu ko maza in za su yi aure, sun fi son mace da ta iya sana’a.

 

Dalilin da yasa na rungumi sana’o’i ke nan:

Kamar yadda na fada a baya, na kasance cikin kungiyoyi da daman gaske, don haka na rungumi harkokin kungiyoyi ne saboda ni mace ce mai son hulda da jama’a kuma ni mace ce mai son tallafawa marayu da gajiyayyu. Domin ana samun matsala a yayin da mutum ya takaitu da rayuwarsa ko ta makusantansa kadai, saboda akwai mabukata da yawa wadanda suke bukatar tallafinmu a koda yaushe. Don haka na rungumi kungiyoyin tallafawa marayu da gajiyayyu da wayar da kan matasa kan illolin shan miyagun kwayoyi da koyawa

matasa sana’o’i da sauransu.  

 

Nasarori:

Na samu nasarori da dama ta inda ban taba tunanin zan samu ba. Nasara ta farko ita ce cigaba da karatu. Haka kuma na sami nasarori da dama a sana’o’in hannu da na ke yi, domin iya sana’a a wajen mace ba karamar nasara ba ce. Hakazalika na sami nasarori a kungiyoyin da nake ciki. Domin ada ban san kowa ba, amma ta dalilin kungiyoyin da na shiga yanzu na san mutane da dama. Haka kuma na sami nasarori da dama wajen tallafawa marayu da gajiyayyu. Don haka a kowanne lokaci na ke godiya ga Allah.

 

kalubale:

Duk wanda ya kasance yana samun karuwa da daukaka dole ne ya fuskanci kalubale daban-daban, daga abokai ko ‘yan uwa da dai sauransu. Amma ni a gaskiya ban sami kalubale ta gida ba. Saboda ina da cikakken goyan baya daga gida. Sai dai in ce na sami kalubale daga abokai da sauran wasu mutane da muke tare da su.

 

Yadda mata suka rungumi sana’o’i a Najeriya:

A gaskiya yanzu mata a Najeriya, sun tashi wajen kama sana’o’i a. Domin yanzu mata da yawa sun gane cewa kama sana’a yana da matukar mahimmanci. Don haka yanzu matan aure da ‘yan mata kowa ya kama sana’a, domin ya tallafawa kansa da sauran wadanda yake tare da su. Saboda haka yanzu mata sun gane su jira ayi masu akwai matsala, don haka sun tashi su kama sana’a domin shi ne mafita a gare su.

 

Abin da na so in yi lokacin da nake karama:

A gaskiya a lokacin da nake karama na so na yi aikin jarida ne, kuma har yanzu ina son na yi wannan aiki na jarida.

 

Tufafin da na fi so:

Ni ma’abociyar atamfa ne da leshi ta fuskar shiga. Ina son su kwarai da gaske.

 

Abincin da na fi so:

Na fi son shinkafa da miya sai kuma tuwo da miyar kubewa danya.

Abin da nake son a rika tunawa da ni:

Ina son a rika tunawa da ni a matsayin mace mai iya zamantakewa da kuma kyautata wa al’umma.

 

Shawara ga mata:

Mata su zamo masu kishin kansu da tsare mutumcin kansu kuma masu neman na kansu ta hanyar kama sana’a. Ya kamata ace kowace mace ta daure ta kama sana’a ko a cikin gida ne. Kuma mata su kasance masu tallafawa na kasa da su. Su daina girman kan cewa su sun fi karfin su yi wani abu. Su tallafawa mazajensu su tallafawa ‘ya’yansu su tallafawa ‘yan’uwansu da sauran mutanen da suke tare da su.