✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar babbakar kan dabbobi ta yi mini komai – Lawan Ahmed

Lawan Ahmed matashi ne da ya bayyana sana’ar babbakar kan dabbobi da yake rike yi a Kasuwar Nama da ke Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa a…

Lawan Ahmed matashi ne da ya bayyana sana’ar babbakar kan dabbobi da yake rike yi a Kasuwar Nama da ke Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa a Kalaba, Jihar Kuros Riba, cewa  ta yi masa goma ta arziki, inda ya ce babban burinsa ya bunkasa sana’ar ta yadda shi ma wani zai so ya koya a hannunsa. A tattaunawarsa da Aminiya ya bukaci Gwamnatin Jihar Zamfara ta kawo karshen kashe-kashen da suka addabi jihar domin harkokin kasuwanci da sana’a su kankama:

Yaushe ka fara sana’ar babbakar kan dabbobi?

Na fara ta ce shekara bakwai da suka gabata.

Me ya jawo hankalinka ka  kama wannan sana’a?

Gaskiya abin da ya sa, saboda yawanci ana yankan dabbobi a nan kasuwar kuma ana babbakar kawunan dabbobin.

Nawa kake babbakar kan saniya kuma nawa ne na rago da sauran kananan dabbobi?

Na farko a wannan  kasuwar an fi yanka raguna da sauran kananan  dabbobi irin su akuya da tunkiya su farashin su ana yi a kan Naira 100 ne. Na saniya kuma kowane kan saniya ana babbakarsa ne a kan Naira 800. Jelar saniya kuma Naira 300 kafar saniya ita ma Naira 300.

Ka taba yin wata babbakar da ta jefa ka cikin matsala tsakaninka da wanda ya kawo maka aikin?

Gaskiya a’a, sai dai yanayin idan an yi ruwan sama ne kawai abubuwa suka jike, to gaskiya a lokacin muna fuskantar matsala itacen da muke hura wuta ya jike ga shi kuma an kawo maka aiki mai aikin na jira idan gashin dabbar ma ta jike shi ma yana zame mana matsala. Shi ne yake da wahalar babbaka.

Wane irin kalubale kake fuskanta a wannan sana’a?

Gaskiya sai dai rashin biya daga masu ba mu aikin ne kawai matsalar, wadansu kan ki biyanmu hakkinmu.

Wace babbaka ce ka yi wadda ka yi farin cikin ba za ka taba mancewa da ita ba?

A koyaushe ma tana zuwa amma ta kwangila wadda ake kawo mana daga waje mu yi ta fi dadi.

Burinka a wannan sana’a?

Burina in kara hakuri, kuma in kara samun ci gaba .

Kana da iyali?

Eh! Kwarai kuwa  ina da mace daya da ’ya’ya biyu.

Ga sana’o’i nan daban-daban ana yi amma sai a ga matasa na raina sana’a me za ka ce ga irin wadannan matasa?

Gaskiya ina kira ga irin wadannan matasa su gane cewa ita sana’a duk karancinta a yi hakuri a rike ta saboda a samu dogaro da kai a daina raina sana’a akwai rufin asiri a ciki.

Kana da burin ka bunkasa wannan sana’a taka nan gaba?

Kwarai da gaske.

Tsakanin babbaka da itace da ta na’urar  zamani wacce ta fi sauki ko wahala?

Ta itace ta fi wahalarwa musamman idan ita ce ba mai cin wuta ba ne, ko kuma idan damina ta kama ya jike. Wanda yake babbaka da itace kafin ya babbake kai biyu kai da kake yi da inji ka babbake  biyar.

Tun daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu kwalliya tana biyan kudin sabulu?

Alhamdulillahi sosai gaskiya.

Za ka so ’ya’yanka idan sun taso su gaje ka a wannan sana’a?

Ka san ita sana’a da karama take zama babba, ko ni kaina ina son in wuce nan, in kai matsayin da ya fi wannan .

Ka taba neman tallafi daga gwamnatin jiharku ta Zamfara ko karamar hukuma don bunkasa wannan  sana’a?

Babban abin da nake so gwamnatinmu ta kawo mana, shi ne ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jiharmu. Yanzu ta zaman lafiya nake yi ba ta neman a taimaka mini ba. Matukar muka samu zaman lafiya sauran bayanai duk masu sauki ne.