Search
Subscribe
Sana’ar faskare ta rufa min asiri – Rabi’u Mai Faskare

Sana’ar faskare ta rufa min asiri – Rabi’u Mai Faskare

Rabi’u Sani wani matashi ne da ke yin sana’ar faskare a Unguwar Fagge a birnin Kano da ke Jihar Kano a tattaunawarsa da Aminiya ya ce duk da cewa mutane na yi wa sana’ar faskare kallon kasakanci, a wurinsa sana’ar ta yi masa komai saboda ta rufa masa asiri:

Mene ne tarihin rayuwarka da yadda aka yi ka fara sana’ar faskare?

Ni  dan asalin garin Zangon Daura ne a Jihar Katsina. Na zo Jihar Kano ne don yin karatun allo. Bayan na sauke Alkur’ani shekara biyar da suka gabata sai na fara yin wannan sana’a ta faskare. Kasancewar akwai wani mutum da yake sana’ar faskare a kusa da mu sai na je wurinsa na nuna masa sha’awata ta yin sana’a. Allah Ya taimake ni sai ya zama ya karbe ni hannu bibbiyu ya koya min sana’ar har yanzu kuma muna tare da shi muna ci gaba da gudanar da sana’armu.

Wanda zai yi sana’ar faskare me yake bukata?

Ita sana’ar faskare ba wani abu ake tanadar mata ba bayan gatari sai karfin jiki. Kodayake sana’ar faskare ba kawai karfi take bukata ba, tana bukatar amfani da tunani da basira wajen aiwatar da ita. Ba karfi ne kawai yake aiki ba, domin sai mutum ya yi amfani da dabararsa wajen sanin yadda zai bullo wa itacen da zai faskara. Da farko sai mutum ya kalli itacen da kyau ya gano ta wane wuri zai

fara sararsa. Da zarar mutum ya lakanci hakan, shi ke nan faskare ba zai yi masa wahala ba.

Wace nasara ka samu a wannan sana’a ta faskare?

Duk da cewa ba zan iya cewa na yi gida da wannan sana’a ba, amma fa wnnan sana’a tana rufa min asiri kwarai da gaske. Babu abin da ba na yi da ita. Ina biya wa kaina bukatuna har ma da na wadansu da ke kusa da ni. Duk lokacin da zan je gida nakan yi wa iyayena da ’yan uwana hidima da wannan sana’a, bayan abin da nake aika musu lokaci zuwa lokaci .

Kin ga a wannan sana’ar wata rana ina samun Naira dubu uku idan na yi aiki tun daga safe zuwa yamma. To abin da nake samu a kudina ya danganta daga irin itacen da na yi aiki a kansa. Idan itacen mai wuya ne ma’ana mai wuyar faskarawa ne, to kudinsa ya fi yawa. Haka kuma ya danganata da lokacin da na fara aikin idan na zo da wuri na fara to zan iya samun kudi mai yawa.

Mene ne kalubalen wannan sana’a?

Kalubale ko in ce matsalar wannan sana’a ba ta wuce ta samun rauni idan tsautsayi ya gitta ba. Duk da cewa a yanzu na kware wajen faskara itacen amma a wasu lokuta nakan ji ciwo musamman a kafa. Amma a yanzu nakan dade wani abu makamancin haka bai faru da ni ba saboda ina kula kwarai da gaske kuma Allah Yana kiyayewa.

Wace shawara za ka ba matasa kan nema na kansu?

Ina kira ga matasa cewa su daina zaman banza, domin shi ke sanya su a hanyar lalacewa. Duk matashin da ya zauna ya ki yin sana’a to dole fa ya dauki na wani. Saboda duk mutum yana da bukata. Abu daya da zai rufa wa mutum asiri shi ne ya nemi na kansa. Mutum ya zauna ya ce ba ya da sana’a wannan karya ce akwai sana’o’i da dama wadanda idan matasa suka karba ba tare da girman kai ba to za su fi karfin su saci abin wani ko su yi bangar siyasa. Ina kira ga matasa ’yan uwana su yi koyi da ni su kama sana’a ko ba sana’ar faskaren itace ba, wata sana’ar ta daban. Idan ya so mutum yana cikin yi, idan Allah Ya kawo masa wata sana’ar sai ya canja, kowa dama yana bukatar ci gaba. Amma fa a sani komai da lokacinsa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin