✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar wanke takalma ta rufa mini asiri –Shu’aibu

Wani mai sana’ar wanke takalmi mai suna Malam Sha’aibu Muhammed ya ce sana’ar wanke takalma tana da matukar muhimmanci domin ta rufa masa asiri inda…

Wani mai sana’ar wanke takalmi mai suna Malam Sha’aibu Muhammed ya ce sana’ar wanke takalma tana da matukar muhimmanci domin ta rufa masa asiri inda yake sauke nauyin iyalansa na yau da kullum.

Malam Sha’aibu ya bayyana haka ne a yayin hira da Aminiya a Kalaba, inda ya ce “A da sana’ar ba a daukarta da muhimmanci, ana raina ta, amma yanzu ga shi an samu sauyin zamani maza da mata za ka samu suna yin sana’ar, wadansu na yin gyaran jaka, wadansu kuma na yin takalma da sauransu.”

Ya ci gaba da cewa “An wayi gari yanzu a Jihar Kuros Riba musamman Kalaba babu sana’ar da ta kai ta haiba. Farko an raina sana’ar an kuma raina mai yin ta, to amma yanzu lokaci ya canja kusan mutane da yawa sun rungume ta. Da wannan sana’ar nake rike da iyalina, kuma ba mu rasa komai ba.”

Da aka tambaye shi ko akwai wani kalubale da yake fuskanta a sana’ar, sai ya ce, “Ai ita sana’a ko kasuwa dole a samu kalubale iri-iri, amma ni babban kalubalena bai wuce na yadda abokan hulda ke kin zuwa su karbi aikin takalmin da suka kawo ba. Domin yanzu haka ina da takalman da suka fi shekara uku masu su ba su zo sun karba ba.”

Amma ya ce duk da irin wancan kalubale hakan bai hana shi samun rufin asiri ba, “Ka ga a cikinta na yi aure na gyara gidanmu na gado a can Arewa.” inji shi.

Malam Sha’aibu ya yi kira ga masu sana’a su rike ta hannu bibbiyu ban da wasa, inda ya ce burinsa shi ne idan ya samu jari ya kara inganta sana’ar ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani.