✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanatoci sun dage zaman da zasu yi akan kasafin kudin 2019

A yau Laraba majalisar dattawan Najeriya ta dage zamanta akan kasafin kudin shekarar 2019 da aka gabatar mata zuwa makon gobe saboda rashin cikakkun bayanan…

A yau Laraba majalisar dattawan Najeriya ta dage zamanta akan kasafin kudin shekarar 2019 da aka gabatar mata zuwa makon gobe saboda rashin cikakkun bayanan da ake da bukata.

A ranar Alhamis da ta wuce ne Kwamitin bin diddigin yadda za a sarrafa kudaden da za a kashe a kasafin kudin 2019, wanda Sanata Mohammed Danjuma Goje ke jagoranta suka gabatar da rahoton kwamitin su a gaban zauren majalisar.

A yau bayan da kwamitin suka rahoton su ga zauren majalisar sai suka gano cewa, ba bu cikakkun bayanan abin da kasafin kudin 2019 ya kunsa.