Search
Subscribe
Sarautar Fawa amanace ce a masarautar Katsina – Sarkin Fawa Usman   

Sarkin Fawa Usman

Sarautar Fawa amanace ce a masarautar Katsina – Sarkin Fawa Usman   

Sarautar Fawa ta samo asali  ne lokaci mai tsawo. Mahauci ko Barinje yana gudanar da wannan sana’a ta sayar da nama ko dai a danyensa ko kuma gasasshe da sauran hanyoyin sarrafa nama don sayarwa.

Alhaji Usman Sa’idu Tudun ’Yanshanu shi ne Sarkin Fawan Masarautar Katsina ya baiyyana yadda sana’ar take da kuma aikinta a masarautar.

“Ita dai sarautar Sarkin Fawa sarauta ce wadda ke da dogon tarihi wadda duk garin da za ka je za ka samu akwai wannan sarauta ta Fawa, sai dai wata na saman wata. Wato duk garin Hakimi ko Magaji za a tarar akwai wannan sarauta,” inji shi.

Sarkin Fawan ya ce, sarautar tana daya daga cikin sarautun da ake nada wa wadansu masu sana’ar gargajiya, irin su kira da fawa da noma da sauransu. “Mu a nan Katsina, wannan sarauta amana ce a tsakaninmu da Sarki da Masarauta. Dalili shi ne, lura da irin yanayin sana’ar tamu ta mu’amala da nama wanda kusan zai yi wuya a ce mutun ya yi mako ba tare da ya ci nama ba, sai fa rashin lafiya. Ka ga kullum sai an yanka dabba domin a samar da nama ga jama’a.  To a kan haka ne, Sarki ke nada Sarkin Fawa ya kuma damka masa amanar kula da mahautan da ke sayar da nama domin su sayar da lafiyayyen nama. Kuma wanda aka yanka bisa shari’a. Shi ne kuma zai kula da batagarin da ke yi wa sana’ar shigar-burtu domin bata ta. Sannan duk wata matsala wadda ta taso a tsakanin mahauci da mai dabba, Sarkin Fawa ne ke shiga tsakani,” inji shi.

Alhaji Usman ya ci gaba da cewa, wannan sarauta a duk inda aka gan ta, to nadi aka yi ba zabe ba, sai wanda ya gaje ta ake nadawa kuma ana yin wannan nadi daga hannun masarautu na gargajiya. “Ni din nan, na gaje ta ce daga iyaye da kakanninmu; na gaji dan uwana wanda Allah Ya yi wa rasuwa wanda shi kuma ya gaje ta daga wajen mahaifinmu kamar yadda shi ma mahaifin namu ya gado daga nasa mahaifin,” inji shi.

“Sarkin Fawa Gambo wanda shi ne ya haifi Sarkin Fawa Dauda, shi kuma ya haifi Sarkin Fawa Sa’idu, shi ne kuma ya haifi Sarkin Fawa Nura, wato yayana wanda bayan rasuwarsa ne aka nada ni. Haka abin ya taho a kuma cikin wannan unguwa tamu da ake kira Tudun ’Yanshanu. Kuma ni ne shugaban duk wani Sarkin Fawa da ke karkashin Masarautar Katsina,” inji shi.

Ya ce yana daga cikin abin da aka sani cewa duk wata sarauta ta gargajiyar da aka nada akwai wasu abubuwa na al’ada da ake yi, inda

Sarkin Fawa Usman ya ce, “Idan ka shigo bangarenmu na mahauta har yanzu ba mu bar al’adunmu ba. Dalilin da ya sa tun baya mutane suke daukar mahauta wadansu irin mutane na daban. Abu na farko da har yanzu muna nan rike da shi shi ne, girmama na gaba. Duk abin da mahauci ke yi da zarar na gaba da shi ya yi masa magana, to yana saurarawa. Sannan ita sana’ar ba kamar saura take ba, in dai ba dan gado b ane, to kana fara yin ta za ta nuna ka, ba kamar sauran sana’o’i ba. Sannan duk inda aka ce za a nada Sarkin Fawa to al’ada ce duk inda wani Sarkin Fawan yake a wannan yankin sai ya zo wajen wannan nadi. Kumar al’adar hawan kaho sai dan gado, domin Allah Ya ba mu sanin dabba da yadda za mu sarrafa ta.”

“Ga kuma Rawar Turu. Wannan rawar duk wanda ya yi ta, in ba mahauci ba ne, to sai ta nuna shi. Ga wasan dambe wanda daga wajen mahauta aka san shi. Sannan akwai wani kidi da ake yi da zarar Sarki ya nada Sarkin Fawa, in ba an yi nadin ba ba a yin wannan kidi. Sai kuma wukar da ake ba wanda aka nada. Sannan ana sanya masa alkyabba da jar dara, amma nan sai in Sarki ne ya yi wannan nadi, misali kamar yadda aka yi min a nan Masarautar Katsina wadda Mai martaba Sarki Abdulmumini ya yi. A takaice dai, shi Sarkin Fawa wakili ne ga masarauta,” inji shi.

Kasancewar sarautar ta samo asali ne daga wata dadaddiyar al’ada, an kuma san akwai wasan barkwanci a tsakanin masu irin wadannan tsofaffin sana’o’i, Sarkin Fawa Usman ya ce, “Ka ga abokan wasanmu su ne masunta, wato masu sana’ar kifi, sannan ga su kansu Fulanin da muke sayen dabbobin a wajensu. Sai kuma masu sana’ar jima. Ba zan manta da wani abin da ya taba faruwa a tsakanina da wadansu majema ba. Na je inda suke sai suka taso min kamar za su cinye ni da surutai iri-iri. Sai na ce, ina so su ba ni Bagaruwa, ai fa nan aka yi tsit, sai wani ya ce, to ni in ba su nama nan take na dubi daya daga cikin wadanda muka je wajen tare na ce, ba su nama, ya sa hannu a aljihu ya fiddo danyen nama ya mika musu. Haka abin yake a sashin Fulani. Duk abin da daya ya amsa daga wajen dayan bai daga kai ya duba.”

To sai dai akwai wani abu ga dukk wanda za a ce yana jagorantar jama’a, wato fuskantar wasu ’yan matsaloli.

Sarkin Fawa Usman ya ce, shi a nasa bangaren matsalar ta jama’arsa ne, wato tsadar dabbobi. Sarkin ya yi nuni da cewa, kowane irin kayan sana’a za a iya samun hawan farashi amma ban da sana’ar fawa.

“Yau kana iya sayo dabba Naira dubu 100, ka sayar da misali kilo a kan Naira dubu. Gobe in ka koma, irin wannan dabbar za ka saya Naira dubu 110 har zuwa da Naira dubu 120 amma kudin kilon yana nan yadda yake. Mutane sun yarda da sauran sana’o’i suna hawa suna sauka amma ban da ta fawa. In yau za ka sayi nama kilo Naira dubu daya ka dawo gobe a ce maka da dari daya sai ka yi tsokaci. Amma in magi ne ko gari aka ce ya tashi, abin da kawai mutum zai ce shi ne, ai yanayi ne, to shi naman ko ita dabbar ba ta da yanayi? Sannan, satar dabbobi da aka rika yi barkatai kafin gwamnati ta shigo, ta haifar da matsalar karancin nama sosai saboda babu dabbobin, amma yanzu alhamdulillahi,” inji shi. A karshe Sarkin Sa’idu ya yi kira ga mahauta su rika sa tsoron Allah a cikin sana’arsu wadda ba su da abin alfaharin da ya wuce ta.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin