✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Dubai ya gurfanar da matarsa a gaban kotun Ingila

A Tsakiyar makon nan ne daya daga cikin manyan hamshakan shugabanni masu dukiya da matsayi a Gabas ta Tsakiya ya kai karar matarsa da suka…

A Tsakiyar makon nan ne daya daga cikin manyan hamshakan shugabanni masu dukiya da matsayi a Gabas ta Tsakiya ya kai karar matarsa da suka samu sabani a gaban wata kotu a birnin Landan.

A shari’ar wadda ta dauki hankalin duniya, Sheikh Mohammed Al-Maktoum, mai shekara 69, wanda shi ne Sarkin Dubai ya kai karar Gimbiya Haya a kan batun kula da ’ya’yansu.

Gimbiya Haya mai shekara 45, wadda ’yar uwa ce ga  Sarkin Jordan, ta tsere daga Dubai zuwa Landan a farkon bana, kuma kawayenta sun ce tana cike da fargaba game da rayuwarta.

Shugabannin kasashen Larabawa suna daga cikin mutanen da a duniya suke tafiyar da harkokinsu na rayuwa cikin sirri, to amma wannan shari’ar tuni ta dauki hankalin duniya.

Sarkin wanda yana daya daga cikin hamshakan masu hannu a gasar sukuwar dawaki ta duniya, yana da dukiyar da ta kai sama da Fam biliyan uku.

Rahotanni sun ce Sheikh Mohammed yana da ’ya’ya 23 da ya haifa da mata daban-daban.