✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Ile Ife ya kwanta dama

A ranar Litinin da ta gabata ce aka sanar da rasuwar Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali. Sanarwar ta fito ne daga Fadar Sarkin…

A ranar Litinin da ta gabata ce aka sanar da rasuwar Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali. Sanarwar ta fito ne daga Fadar Sarkin inda ta yi bayanin cewa, ya rasu ne a wani asibiti a garin Ile-Ife a Jihar Osun.

Marigayi Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali ya rasu yana da shekara 72 ya bar mata da ’ya’ya 16 da jikoki.

Ya hau karagar sarautar ce a 1990 lokacin da ya gaji Sarkin Hausawa Alhaji Isyaku Yaro Gangariya. Sarakunan Hausawan garuruwa daban-daban a Jihar Osun ne suka jagoranci al’ummarsu zuwa wajen jana’izar marigayin wadda aka gudanar a karkashin jagorancin Na’ibin Babban Limamin Masallacin Sabo Ile-Ife, Malam Ja’afaru Kawu.