✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ga Tambuwal: Ka sallami duk jami’i mai wasa da aiki

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji  Aminu Waziri Tambuwal ya kori duk wani jami’insa da ya…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji  Aminu Waziri Tambuwal ya kori duk wani jami’insa da ya tsaya yana wasa da aiki domin wanda yake haka ba masoyin jihar ba ne.

Sarkin Musulmi ya yi wannan kalami ne lokacin da ya kai ziyarar Barka da Sallah ga Gwamnan a fadar gwamnati a ranar Talatar da ta gabata. Ya yi kira ga shugabannin  jihar su rika bambanta harkar zabe da shugabanci, lokacin zabe ya wuce su hadu a yi aiki tare don ci gaban jihar.

Ya gode wa gwamnatin Tambuwal kan kokarin da take yi ga harkar tsaro a jihar, kuma ya nemi gwamnati ta ci gaba da matsa kaimi don dorewar tsaro.

Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta kwaikwayi salon bayar da tallafi ga kanana da matsakaitan ’yan kasuwa irin na kasar Indonesiya.

Gwamna Tambuwal ya ce lokacin da ya kai ziyara a kasar ya gano shirye-shirye masu kyau da zai dabbaka domin amfanin jama’arsa.

Ya ce zai inganta Hukumar Zakka da Wakafi yadda za ta guje wa tsunduma cikin harkar siyasa, za a shigo da mutanen da ba ruwansu da harkar siyasa.

Gwamnan ya ce zai samar da ayyukan yi da matasa za su shiga cikinsu sosai, wanda za a ga alfanun shirye-shiryensu nan da shekara hudu masu zuwa. “Muna farin cikin yadda harkar tsaro ta inganta a Jihar Sakkwato za mu kara kaimi don ganin an ci gaba da samun zaman lafiya a jihar nan,” inji shi. a cewar Tambuwal.