✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau: Gwamnatin Kaduna ta karbi sunaye uku

Gwamnatin Jihar ta karbi sunayen ’ya'yan sarki uku domin zabar Sarki na 19

Gwamnatin Jihar Kaduna ta karbi sunayen ’ya’yan sarki guda uku da za ta zabi sabon Sarkin Zazzau daga cikinsu.

Majalisar zabar Sarkin Zazzau ta gabatar wa gwamnain jihar sunayen ne bayan rasuwar Sarkin Shehu Idris a ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 bayan shekara 45 a kan karagar mulkin masarautar.

Takardar bayan taron tantance masu neman sarautar da Aminiya ta samu ta nuna cewa sunayen da masu zabar sarkin suka mika wa gwamnatin jihar su ne: Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu; Yariman Zazzau, Alhaji Mohammed Munir Ja’afaru da kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris.

Zaman da ya gudana ranar Alhamis a Zariya kan batun zabar Sarkin Zazzau na 19 ya samu halarcin masu zabar sarkin masarautar da suka hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu; Fagachin Zazzau, Alhaji Umaru Muhammad; Makama Karamin Zazzau, Alhaji Muhammad Abbas; Babban Limamin Zazzau, Alhaji Dalhatu Kasimu Imam da kuma Limamin Konan Zazzau, Alhaji Muhammad Sani Aliyu.

Sai dai Magajin Garin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali, wanda makusanci ne ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba ya daga cikin wadanda ake neman nadawa Sarkin Zazzau.

Masu zabar sarkin sun tantance tare da ba da maki ga ’yan takarar ta hanyar la’akari da cancantarsu, kwarewa a hakimicin da suka rike, kyawun hali, kyautar girmamawa ta kasa, iya sasanta tsakanin mutane da kuma lafiyar jiki.

A sakamakon tantancewar da masu zabar sarkin suka yi, Iyan Zazzau ya samu maki 88, Munir Ja’afaru, 87 sai kuma Aminu Shehu Idris, maki 53.

Mutum ukun su ne kadai aka ba wa maki, kuma dukkannin masu zabar sarkin sun sanya hannu a takardar da aka aike wa gwamnan jihar.

Rahotannin da muka samu Juma’a da dare sun nuna masu zabar sarkin sun yi zama da jami’an gwamnatin a Gidan Gwamnatin Jibar Kaduna.

Mutum 11 ne daga gidajen sarautar Zazzau hudu suka gabatar wa masu zabar sarkin bukatunsu na zama Sarkin Zazzau na 19.

Gidajen sarautar Zazzau su ne gidan Katsina wanda daga nan Sarki Shehu Idris ya fito. Sai gidan Barebari, Mallawa da na Sullubawa.

Sauran ’yan takarar su ne: Mai Shari’a Tanimu Zailani, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali, Mu’azu Aliyu Ahmed, Alhaji Sa’idu Mailafiya, Arc. Mohammad Aminu Idris, Adamu Umaru Idris, Alhaji Shitu I. Dikko, da kuma Alhaji Abdulkarim Aminu.

Iyan Zazzau

Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu ya fito ne daga gidan Katsinawa.

Iyan Zazzau wanda ya fi yawan maki an haife shi ne a 1951, lokacin mahaifinsa, Muhammadu Aminu na Sarkin Zazzau.

Kwararren akanta ne kuma attajiri, sannan shi ne Hakimin Sabon Gari na farko, matsayin da ya rike daga 1979 zuwa 2018.

Yariman Zazzau

An haifi Munir Ja’afaru wanda lauya ne kuma kwararre a gudanarwar harkokin gwamnati da kamfanoni ne a watan Maris, 1956.

Shi ne na biyu wajen yawan maki kuma ya fito ne daga gidan Barebari.

Turakin Zazzau

Alhaji Aminu Shehu Idris da ne ga marigayi Sarki Shehu Idris.

An haife shi a sheakarar 1976; shi ne na uku wurin yawan maki kuma ya fito ne daga gidan Katsinawa.