✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau ya kai ziyarar farko ga Sarkin Musulmi

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya kai ziyararsa ta farko fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III. A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya…

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya kai ziyararsa ta farko fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya bukaci wadanda suka nemi sarautar Zazzau da ba su samu ba, da su hada kai da wanda Allah Ya ba wa sarautar domin ciyar da masarautar gaba.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya furta hakan ne lokacin da ya karbi tawagar sabon Sarkin a fadarsa dake Sokoto

An kuma tsayar da ranar 9 ga watan Nuwamba na 2020 a matsayin ranar bayar da sandar girma ga sabon sarkin na 19 a Masarautar Zazzau.