✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Kiyaye Ka’idoji

Na tsaya a zango na uku na wannan makala ta ‘Sarrafa Albarkatun Gona’ inda, kamar a sauran zanguna biyu na baya na makalar na tattauna…

Na tsaya a zango na uku na wannan makala ta ‘Sarrafa Albarkatun Gona’ inda, kamar a sauran zanguna biyu na baya na makalar na tattauna irin albarkatun gonar da dan kasuwa zai iya samu ya sarrafa a shiyyar Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Idan mai karatu bai manta ba makala ta farko da ta biyu na yi bayanai akan ire-iren albarkatun gona da dan kasuwa zai iya samu daga shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso gabas domin sarrafawa ya sayar a kasuwannin ciki da wajen kasar nan.

Haka kuma idan mai karatu na biye da ni, na yi bayanin daukar irin wadannan albarkatu domin fadakar da dan kasuwa irin bukatar da ake da ita a kasuwannin gida Najeriya da kasuwannin kasashen waje, walau kasuwannin kasashen da ke makwabtakarmu ko kuma ma na kasashen ketare. Na kuma ce zan yi bayanin siffar yadda masu bukatar irin wadannan albarkatu ke bukatarsu da kuma ka’idojin da masu saye ke bukatar samunsu. Na kuma yi alkawarin ba dan kasuwa shawarwari a kan inda zai samu wadannan albarkatun gona, da yadda zai sarrafa su domin karbuwarsu a wadannan kasuwanni.
Na kuma ce zan bayar da hasken wuraren da ake bukatar kowace haja a cikin gida Najeriya ko kuma kasashen da ake bukatarta a duniya. Sannan kuma in duba tallafin da dan kasuwa zai iya samu dangane da irin abin da zai fitar ya zuwa kasashen duniya.
Kafin in fara daukar wadannan albarkatun gona da daidai da daidai in yi wadannan bayanai a kansu, a wannan mako zan fara bayar da hasken ka’idojin da dan kasuwa yakamata ya yi hattara da su, wadanda suka jibanci dukkanin albarkatun gonar da zai sarrafa domin sayarwa a kasuwannin gida da na waje.
Abu mafi mahimmanci da dan kasuwa zai kaddara a zuciyarsa yayin shiga wannan harka shi ne, masu sayen kayansa wadansu mutane ne masu bin ka’ida kwarai da gaske wajen sayen irin wadannan kayayyaki. Na farko dai, kamar yadda na fadakar a mukalun baya, mafi yawancin kasashen duniya, musamman ma kasashen Turai da na Amurka na hana shigar kayayyakin da ba a bi ka’idar shiga da su ba. Irin wadannan kai’doji sun hada da irin samfurin kayan da ake bukata da yadda aka bukaci a tsaftace su da kuma bin ka’idar irin mazubin da aka nemi a saka su. Wata karin ka’idar da kasashen suka tsayar ita ce ta mizani; misali, kilo nawa-nawa aka amince da a saka doya a mazubi, ko garin alabo ko na masara. Ko kuma lita nawa-nawa ya kamata a zuba man ja ko na gyada a mazubinsu.
Wata ka’ida kuma ta fitar da irin wadannan kayayyaki zuwa kasashen ketare ita ce ta buga takardar bayanin kayan (wato lebel da Turanci) a kan kowane mazubi. Irin wannan ka’ida na iya tasowa daga mai sayan kayan ko kuma daga hukumar kasar da kayan zai shiga. Wadannan bayanai sun hada da sunan kayan da kuma ranar da aka zuba shi, da kuma ranar da ake tsammanin zai daina amfani. Wadansu lokutan a kan bukaci a buga daga wane gari kayan suka fito, a wace kasa, kuma wa za a kai wa, kuma a wane gari yake. Wani lokaci a kan bukaci tabbacin mai kula da kaya irin wadannan, wato cukuman (Produce Inspector a Turance), inda zai sa hannu cewa kayan sun cika dukkanin ka’idojin da aka tsayar musu.
Rashin bin ka’idojin fitar da kaya kasashen waje ya jawo wa ‘yan kasuwarmu asarar kudi da ta abokan hulda masu yawa. Akwai wani lokaci a shekarun baya da aka kaskantar da farashin kokon da ya fito daga Najeriya saboda rashin tsabtace shi. Wannan ya faru ne saboda samun duwatsu da sauran tarkacen gida da na gona a cikin buhunan kokon da aka saya daga Najeriya. Saboda haka idan farashin koko a duniya na dalar Amurka 100 kowane kilo a misali, sai a sayi kokon Najeriya a kan dala 80, domin tunanin algus din da za a iya samu a cikinsa da kuma rashin tsaftace shi. Amma saboda cika ka’ida aka rika sayen kokon da ya fito daga Ghana da wanda ya fito daga kasar Kwaddebuwa a kan farashin duniya.
Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu mako na gaba.