✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar mutane: Mazauna kauyukan Abuja na hijira zuwa birane

Matsalar satar mutane da ta addabi wasu yankunan Abuja ta sa jama’a daga wasu kauyukan da lamarin ke shafa na hijira zuwa biranen da ke…

Matsalar satar mutane da ta addabi wasu yankunan Abuja ta sa jama’a daga wasu kauyukan da lamarin ke shafa na hijira zuwa biranen da ke kusa da su.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa matsalar ta fi shafar kauyukan kananan hukumomin Abaji da Kuje da Kwali ne a cikin kananan hukomomi shida na Abuja, kuma yankuna uku na kan hanyar Abuja ne zuwa Lakwaja a Jihar Kogi.

Haka Aminiya ta gano cewa wadansu da matsalar ke shafa kamar Fulani makiyaya na barin daukacin yankin Birnin Tarayya ne zuwa wasu jihohi tare da dabbobinsu.

Ko a wannan mako wadansu da ke dauke da bindigogi sun kai hari a kauyen Kabi-Mangoro da ke Karamar Hukumar Kuje, yankin da matsalar ta fi kamari, inda suka kashe mutum hudu mace daya da maza uku.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 9 saura na dare inda suka bude wuta a kan uku daga cikin mutanen da ke zaune a kofar gidansu bayan sun yi yunkurin tserewa, yayin da macen kuma harsashi ya same ta a cikin gida.

Sai dai a bayanin Rundunar ’Yan sandan Abuja ta ce mutum biyu ne suka rasu a lamarin. Bayanin na ’yan sanda ta bakin Kakakin Rundunar, ASP Mariam Yusuf ta ce jami’ansu daga babban ofishinsu na kauyen Pegi da ke yankin sun samu nasarar kama mutum biyu daga cikin maharan bayan an ankarar da su.

Haka a cikin watan  Disimban da ya gabata, wadansu ’yan bindiga da adadinsu ya kai 20 sun yi ajalin wani magidanci mai suna Usman Dadonyi lokacin da suka kai hari a kauyensu na Sukuku da ke Karamar Hukumar Kwali, sannan suka yi garkuwa da dansa.

Bayanai sun ce da farko ’yan bindigar sun samu dan mutumin ne mai suna Nasiru Usman a cikin shagonsa na cajin waya da ke kofar gidansu suka bukaci ganin mahaifinsa. “Yaron ya yi musu bayanin cewa mahaifinsa baya nan, sai dai bayan sun yi masa barazanar za su kashe shi idan bai kai su inda mahaifinsa yake ba. Nan take ya kai su wajen mahaifin cikin fargaba. Bayan magidancin ya kula da mutanen sai ya yi yunkurin gudu kuma nan take suka bude masa wuta ya rasu,” inji majiyarmu

Haka kwana biyu kafin ranar Kirsimeti an sace wani kane ga Shugaban Karamar Hukumar Abaji, mai suna Auwal Ajiya tare da wadansu mutum hudu da suka shiga mota tare.

Wani dan uwan matashin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce matashin wanda ya shiga motar haya daga garin Abaji da misalin karfe 6 na safe da niyyar zuwa kauyen ’Yangoji da ke Karamar Hukumar Kwali, wadansu da ke dauke da bindiga sun tsayar da motarsu a kusa da kauye Kamadi da ke hanyar Abuja zuwa Lakwaja, inda suka wuce da su cikin daji.

A bangaren makiyaya wadanda yawancin masu satar jama’ar daga cikinsu suke, binciken Aminiya ya gano cewa su kansu ba su tsira daga matsalar ba, saboda ’yan bindigar na zuwa rugagensu suna dauke mutane tare da kora dabbobinsu.

Wani jagoran Kungiyar Miyetti Allah a Birnin Tarayya Abuja, ya ce ko kamar mako daya da ya gabata an sace mutum hudu a wata ruga da ke Karamar Hukumar Kwali. Ya ce an sace mutanen ne a kauyen Yibu da ke yankin, ciki har da wani dattijo mai suna Alhaji Nyaro. Ya ce an biya kudin fansa Naira miliyan shida a kan mutumin kafin a sako shi.

Jagoran na Miyetti Allah ya ce sakamakon wannan matsala, al’ummar yankunan na komawa cikin garuruwa, yayin da Fulani makiyaya da ba za su iya zama a cikin gari ba saboda dabbobinsu, ke hijira daga yankin na Birnin Tarayya zuwa wasu jihohi.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa an samu saukin matsalar a hanyar Zuba zuwa Suleja inda a baya aka yi ta tare jama’a musamman da maraice zuwa dare a tsakanin Dutsin Zuma zuwa Suleja ta bangaren babbar hanya da ta nufi Kaduna.

Wasu majiyoyi sun ce hakan ba zai rasa nasaba ba da girke karin sojoji a kusa da yankin da aka yi fama da matsalar ba.