Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Saudiya ta kammala karbar matakin farko na mahajjatan bana miliyan 1.8

Babban Daraktar Fasfo na kasar Saudiya, ya ce kasar ta kammala karbar rukunin farko na mahajjatan bana ta kasa da ruwa da ma ta sama.

A yayin wani taron manema labarai a birnin Jedda, da aka yi yau Laraba, Daraktan, Manjo Janar Sulaiman Bn Abdul-Aziz Al Yahya, ya bayyana cewa, ya zuwa karfe 12 na yau, maniyata kimanin miliyan 1,819,790 sun riga sun shiga kasar dan gudanar da ayyukan Hajjin bana.

ADVERTISEMENT

Bayanan sun nunar da cewa, mahajjata miliyan 1,708,152 ne suka shiga kasar ta tashoshin jiragen sama, yayin da dubu 94,388 suka shiga kasar ta tashoshin mota; sai kuma mahajjata dubu 17,250 da suka isa ta tashoshin ruwa.

ADVERTISEMENT