✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura kiris in mutu saboda kwankwadar barasa -Mike Tyson

Shahararren dan damben boding da ke Amurka Mike Tyson ya ce da alama ya kusa mutuwa ganin yadda yake kwankwadar barasa babu kakkautawa.dan damben, ya…

Mike TysonShahararren dan damben boding da ke Amurka Mike Tyson ya ce da alama ya kusa mutuwa ganin yadda yake kwankwadar barasa babu kakkautawa.
dan damben, ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata a lokacin da yake jawabi kafin a fara gasar dambe ta ESPN Friday Night Fights.
“Ina son gudanar da rayuwa mai tsafta, ba na son mutuwa amma da alama na kusa mutuwa ganin yadda na saba kwankwadar barasa”.
Tyson ya cigaba da cewa “a lokuta da dama nakan kasance ba ni da da’a sai dai ina rokon a yafe min kurakuran da nake aikatawa da fatan zan canza rayuwa na koma mutumin kirki”.
“A yanzu na kwana shida ba tare da na kwankwadi giya ba, kuma hakan ya zama abin mamaki da al’ajabi a gare ni kuma alama ce ta zan iya bari idan na daure”.
Tun bayan da Mike Tyson ya daina yin dambe ya koma harkokin yi wa kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu yin tallace-tallace ne a fadin duniya saboda suna da daukar da ya samu a fagen wasan damben boding.